Ana yada manhajar da ke dauke da sirrin mutane a Facebook

Woman with calendar Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Menstruation apps track users' fertility

Ana ta yada bayanan sirri da suka hada da sirrin yadda mutane suka yi jima'i na wata manhaja a shafin Facebook, kamar yadda wani kamfani na Privacy International ya fada.

Kamfanin na Privacy International ya gano yadda manhajar ke bibiyar bayanan sirrin mutane, musamman ma a shafukan sada zumunta.

Bayanan diddigin sun gano yadda ake bibiyar halin da mata ke ciki ta fuskar jinin al'ada, da kuma alamomin zuwan sa, baya ga alamar haihuwa.

Tun bayan da masanan suka fara binciken ya sanya wani kamfani mai makamancin wannan manhaja ya yi saurin sauya yadda yake ajiye bayanan sirrin mutane.

Manhajojin jinin al'ada na tattara bayanan sirri da dama na mutane, kama daga lafiyar jikinsu zuwa bayanai na jima'i, yanayin da suke ciki, abinda suke ci ko sha da kuma irin audugar da mata masu al'ada suka yi amfani da ita.

Ta yadda wannan manhaja ke gano bayanan sirrin mutane musamman mata shi ne amfani da ranakun ko kuma watan da suka fara jinin al'ada da kuma lokacin da suke tsammanin zuwan sa.

Hakkin mallakar hoto PI
Image caption PI kuma na wallafa abin da Facebook ya hango

Yadawa a Facebook na faruwa ne ta kafafen sada zumunta, wadanda ke fafutukar samun cunkoson mutanen da za su rika shiga shafukansu, kasancewar hakan na taimaka musu wajen samun kudaden shiga ta hanyar jawo hankulan masu tallace-tallace.

PI ta bankado ire-iren wadannan manhajoji, da suka hadar da na bibiyar jinin al'ada, sai dai irin su Period Track Flo da Clue Period Tracker ne ba su bayyana bayanan sirrin mutane a shafin na Facebook ba.

Amma sauran kamar su Maya da kamfanin Plackal ya kirkira mutane sama da miliyan biyar ne suka sauke akan wayoyin su ta hanyar Goggle Play, sai MIA na kamfanin Mobapp Development imited shi kuma da mutane sama da miliyan daya suka sauke.

Binciken masanan ya ci gaba da cewa manhajar My Period ta kamfanin Linchpin Health sama da mutane miliyan guda ne shi ma suka sauke ta a kan wayoyinsu.

PI ta ce kamfanin manhajar Maya ya tabbatar da cewa ya cire dukkanin bayanan mutane daga shafin Facebook tare da sauye-sauyen gaggawa kan yadda yake adana bayanan.

Wata sanarwa da ya aikewa BBC: "Dukkanin bayanan da manhajar Maya ya tattara suna da muhimmanci sosai ajen gudanar da aiki mai inganci.

"Sai dai bayanan da suka shafi jinin al'ada abu ne da ya dogara da wani yanayi na daban da ba lallai ne a dogara da shi ba.

"Masu amfani da manhajar mu suna sane da ka'idojin mu da kuma tsarin da muke amfani da shi na ajiyar bayanan sirri kafin su yi rijista da Maya. Amma kuma suna iya goge duk wasu bayanan su da suka sanya kafin su yi rijista tun farko."

Hakkin mallakar hoto PI
Image caption Manhajar Maya na karfafa wa masu amfani da ita gwiwa su fadi yanayin da suke ciki sai kuma su yada a Facebook

PI ta kuma ce nauyin da ya rataya a wuyan irin wadannan kamfanoni shi ne, bin tsarin duk wta doka da ta shafi kare hakkin sirrin bayanan jama'a, kasancewar yarda da su ya sanya suke ganin zasu iya ba su amanar bayanansu.

Sai dai kamfanin Facebook ya sanar da cewa zai kaddamar da wasu bangarori da ya kamata masu amfani da irin wadannan manhajoji su shiga domin dakatar da duk wasu tallace-tallace ko kuma bayanai da ake aike musu.

Labarai masu alaka