Hotunan 'yan Najeriyar da aka kwaso daga Afirka ta Kudu

Sawun farko na 'yan Najeriyar da suka tserewa hare-haren kin jinin baki daga Afirka Ta Kudu sun isa birnin Legas a ranar Laraba da daddare.

Bayanan hoto,

Wata mata goye da danta a cikin sawun farko na 'yan Najeriya kenan da suka dawo daga Afirka Ta Kudu, a birnin Legas.

Mutum 188 cikin 600 na 'yan Najeriya da suka iso a sawun farko na 'yan ciranin da suka ce suna sha'awar dawowa gida, bayan hare-haremn kin jinin baki da aka kai a biranen Pretoria da Johannesburg na Afirka ta Kudu.

Sun samu jinkiri na sa'o'i takwas kafin jirginsu ya bar babban filin jirgi na OR Tambo.

Bayanan hoto,

Wani mutum kenan cikin sawun farko na 'yan Najeriya da suka dawo daga Afirka Ta Kudu bayan hatsaniya da aka yi, yayin da yake rera taken kasarsa bayan isowar su Legas.

A cewar jakadar Najeriya na Afirka Ta Kudu, ba a taho da wasu mutanen ba saboda rashin isassun bayanai kan tahowa da yara da suke son yi.

Bayanan hoto,

Mutanen da suka sauka daga jirgin sawun farko kenan na 'yan Najeriya da aka dawo da su daga Afirka Ta Kudu, a jihar Legas

Hargitsin ya jawo durkushewar dangantaka tsakanin manyan kasashen biyu na nahiyar Afirka masu karfin tattalin arziki.

Shugabar hukumar kula da 'yan Najeriya mazauna kasashen waje, Abike Dabiri-Erewa ta ce jirgi na biyu zai tashi zuwa Johannesburg domin kwaso sauran mutane masu son dawowa, zuwa Najeriya.

Bayanan hoto,

Wani mutum kenan yake nuna dan yatsa cikin farin ciki yayin da suka isa Legas a jirgin farko da ya kwaso 'yan Najeriya daga Afirka Ta Kudu bayan hatsaniya da aka yi a can

Mutum 12 ne suka rasa rayukansu a hare-haren kin baki da aka kai wa mutane da kuma kasuwancinsu a Afirka Ta Kudu, ciki har da wasu baki guda biyu.

Duk da cewa Ma'aikatar Hulda da Kasashen Waje na Najeriya ta ce babu dan Najeriyar da ya mutu a harin, labaran bogi da aka yada a shafukan intanet sun tayar da hankulan jama'a.