An ci tarar Gimbiyar Saudiyya kan 'cin zarafin' wani

Yariman Saudiyya mai jiran gado Mohammed Bn Salman Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Gimbiya Hassa kanwar Yariman Saudiyya mai jiran gado ne Mohammed Bn Salman

Wata kotu a kasar Faransa ta yanke wani hukunci na musamman ga Gimbiya Hassa bint Salman ta kasar Saudiyya, tare da cin ta tarar dala dubu 11, sakamakon samun ta da laifin garkuwa da wani mutum da kuma cin zarafinsa.

Kotun ta samu Gimbiya Hassa bint Salman da hannu wajen lakadawa mutumin duka.

Alkalan kotun dai na tuhumar Hassa, wadda 'ya ce ga sarkin Saudiyya da bayar da bawa daya daga cikin masu tsaron lafiyarta umarnin dukan mutumin a wani gidan shakatawarta da ke birnin Paris.

Ashraf Eid wanda aikinsa shi ne gyaran famfo, ya shaida wa 'yan sanda cewa an daure masa hannaye.

Ya ce an lakada masa duka da naushinsa da kuma tilasta masa sumbatar kafafun Gimbiya Hassa.

Ya kara da cewa Gimbiya Hassa Bint Salman na zargin sa da daukar hoton bidiyonta a wayarsa ta salula.

Kotun ta yanke wa Gimbiya Hassa bint Salman hukuncin jeka ka gyara halinka, sakamakon samun ta da laifin garkuwa da ma'aikacin.

Sannan da lakada masa duka a dakin alfarma da ta kama a wani Otal da ke birnin Paris.

Sai dai lauyan da ke kare gimbiyar ya musanta laifin da ake tuhumar ta da ta aikatawa, inda ya ce da dama daga cikin bayanan da ma'aikacin Ashraf Eid ya gabatar wa kotun babu gaskiya a ciki, kuma za su daukaka kara.

Mutumin ya shaida wa masu bincike kan al'amarin cewa an kwace masa wayar salularsa inda aka lakada masa duka.

Sannan aka ce ta mayar da shi kamar kare, tana mai fada masa cewa bari a koya maka yadda ake magana da gimbiya, da kuma yadda za ka rika magana da jinin sarauta"

Gimbiya Hassa bint Salma mai shekara 43 wadda 'yar uwa ce ga yarima mai jiran gado na kasar Saudiyya Muhammad bin Salman, ta musanta tuhumar da ake mata ta bakin lauyoyinta.

Sannan kuma ba ta cikin kotun lokacin da aka yi zaman sauraron karar.

A shekarar 2013 ne wata kotu a kasar faransa ta bayar da umarnin karbe ikon asusun ajiya na Gimbiya Maha al-Sudairi wadda mata ce ga tsohon ministan harkokin cikin gida na kasar ta Saudiyya Nayef bin Abdul Aziz.

Hakan ya biyo bayan gaza biyan makudan kudade da wani Otal na alfarma ke binta bashinsu, adadin da suka tasamma yuro miliyan shida (Dala miliyan 6.7).

Labarai masu alaka