Ba ma leken asirin Amurka - Netanyahu

Donald Trump and Benjamin Netanyahu grasping hands in front of their national flags Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Netanyahu ya kkaryata batun da babbar murya

Firai ministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya fito karara ya yi watsi da rahoton da aka fitar, inda aka ce kasarsa na leken asirin Amurka.

A wata makala ta siyasa da aka wallafa ta ambato tsoffin manyan jami'an Amurka uku da suka bayyana cewa wata na'urar leken asirin da aka gani a gefen fadar White House mallakar Isra'ila ce.

Sai dai a wata sanarwa da Mista Netanyahu ya fitar ya karyata wannan lamarin, inda ya ce zuki ta malle ce zalla.

''Akwai wata yarjejeniya da aka cimma a can baya da ta bayar da umarnin kada Isra'ila ta yi katsalandan kan duk wani abu da ya shafi bayanan sirrin Amurka.''

Wakilan BBC sun tuntubi ma'aikatar harkokin kasashen wajen Amurka domin jin ta bakinsu.

Me sanarwar ke cewa?

An wallafa zargin ne a shafin intanet na jaridar Politico a ranar Alhamis.

Rahoton ya ce an ga wasu na'urori na leken asiri da ke lekawa cikin wayoyin mutane domin tattaro bayanai na wayoyin sadarwa da ke kusa da fadar Shugaban Amurka da kuma wasu sassa na Washington.

Wadannan na'urorin suna aiki ne kamar turakun watsa sabis din waya, inda suke tattaro bayanan sirri game da wayoyin jama'a.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption An ga na'urorin kusa da fadar White House

Daya daga cikin tsoffin jami'an Amurka da ya yi magana da jaridar Politico kuma ya bukaci a sirranta sunansa, ya bayyana cewa da alamu an kera na'urorin ne domin su yi leken asiri ga Shugaba Trump.

Sai dai ya bayyana cewa babu tabbacin ko sun cimma nasarar yin hakan.

Jami'an leken asiri na FBI ta Amurka sun yi kokarin gano inda na'urorin suka fito sai dai sun bayyana cewa da alamu Isra'ila ce take da na'urorin.

Shi dai wannan tsohon jami'in na Amurka da ya shaida wa jaridar Politico wadannan bayanai ya caccaki gwamnatin Trump, inda ya ce gwamnatin ba ta fito fili ko kuma a sirrance ta tsawata wa Isra'ilar ba.

Labarai masu alaka