Ana takaddama kan inda za a binne Mugabe

gawar Mugabe

Iyalin tsohon shugaban Zimbabwe da ya rasu, Robert Mugabe, sun ce sun kadu da suka ga gwamnati ba ta tuntube su game shirye-shiryen jana'izarsa ba.

Mista Mugabe ya rasu ne makon jiya yana da 95.

Ana shirin kai gawarsa wani filin kwallon kafa a Harare, babban birnin kasar, don jama'a su girmama shi.

Akwai dai takaddama tsakanin gwamnatin da iyalinsa game da inda za a yi masa kabari.

Image caption Matar marigayi Mugabe a gidanta da ke Harare

Iyalan Mista Mugabe sun ce za a nuna gawarsa a gidan sa da ke kauyen Kutama a daren Lahadi, kuma za a binne shi a wani bikin sirri da za'a gudanar.

Dubunnan masu nuna alhinin mutuwar sa ne suka yi dafifi a filin wasa na Rufuro domin nuna ban girma ga gawar marigayi Mista Mugabe.

An samu cunkoso sakamakon kokarin mutane na ganin sun bayyana gaban gawar Robert Mugabe. Inji kamfanin dillancin labarai na Reuters.

Trust Nyakabawo ya shaidawa reuters cewa sun kai ziyara filin wasan na Rufaro ne sakamakon cewa: "Muna cikin alhini mutuwar sa, tafiyar sa tayi mana ciwo sakamakon cewa mun saba ganin sa a raye kuma a matsayin san a uban kasa wanda ya jagorance na tsawon lokaci."

Filin wasa na Rufaro ne a nan ne aka rantsar da Robert Mugabe a matsayin shugaban Zimbabwe na farko a shekarar 1980.

"za'a binne gawar sa a kauyen Kutama da daren ranar Lahadiā€¦. Biyo bayan wani kwarya-kwaryan biki da makusantansakadai ne zasu halarta.

Iyalan sa dai sun yanke shawarar cewa ko dai Litinin ko Talata basa bukatar wata ranar tunawa da 'yan mazan jiya. Inji wani dan 'uwa ga marigayi Mugabe da ya shaidawa AFP.

Shugaba Emmerson Mnangagwa ya ayyana Mista Mugabe a matsayin gwarzo na kasa bayan rasuwarsa, yana mai nuna cewa ya kamata a binne shi inda a makabartar da ake binne 'yan mazan jiya.

Labarai masu alaka