Dalilin rashin sako Naziru Sarkin Waka daga gidan yari - Sadiq Kurawa

Naziru Sarkin Waka Hakkin mallakar hoto NAziru Sarkin Waka / Facebook
Image caption Naziru Sarkin Waka

Ana sa ran sakin Sarkin wakar Sarkin Kano, Naziru M. Ahmad daga gidan yari a Kano, bayan shafe daren jiya yana tsare saboda rashin cika sharuddan belin da kotu ta gindaya masa.

Rundunar 'yan sandan jihar Kano ce ta gurfanar da fitaccen mawakin a gaban kotu bisa zargin fitar da wasu wakoki ba tare da izini ba.

Lauyan matashin mawakin Barista Sadiq Sabo Kurawa ya yi wa BBC karin bayani kan halin da ake ciki:

"Abin da ya hana a sako shi jiya shi ne rashin kammala tantance abubuwan da kotu ta gindaya masa".

Ya kuma ce tun jiya "Jami'in kotu da zai tantance sahihancin abubuwan da kotun ke bukata ya riga ya kammala aikinsa".

Wannan na nufin idan alkalin ya amince da cewa ya cika sharuddan, yana iya sako shi cikin yinin Jumma'a.

Amma idan hakan bai samu ba, Naziru Sarkin Waka na iya shafe kwanakin karshen mako a gidan yari har sai ya gamsar da alkali cewa dukkan sharuddan da aka shimfida ya samar da su.

Amma lauyan nasa na da karfin gwuiwar haka ba zai faru ba.

"Alkali ya ce da zarar ya shigo kotu yau Jumma'a, zai duba rahoton jami'in da ya tantance cewa an cika sharuddan, sannan ya sanya hannu kan takardar da za ta ba mu damar karbo Naziru daga kurkuku".

Kotu dai ta ba da belin Naziru bisa sharadin ajiye fasfo dinsa da kudi Naira 500,000 sannan ya gabatar da mutum 3, ciki har da dagaci domin su tsaya masa.

Labarai masu alaka