An fara gwajin rigakafin cutar Maleriya a Kenya

A Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Maleriya tana kashe fiye da mutum 400,000 a shekara

An fara gwajin amfani da allurar rigakafin cutar zazzabin Malaria a Kenya a karon farko ranar Juma'a.

Kenya ce kasa ta uku da ta shiga shirin bayan kasashen Ghana da kuma Malawi.

A yanku nan kasashen uku, ana sa ran yara fiye da 300,000 ne 'yan kasa da shekara biyu za a yiwa rigakafin a kowace shekara.

An kwashe tsawon shekara 30 na bincike kafin samun rigakafin, mai suna RTS,S. Kuma tana aiki ne idan aka dabi'antar da garkuwar jikin dan Adam, domin yaki da kwayoyin cutar, wanda sauro ke yada ta.

Gwajin da aka yi a farko ya nuna cewa kusan hudu daga cikin kowane yara 10 tsakanin shekaru biyar zuwa 'yan wata 17, wadanda aka bai wa kwayoyin maganin hudu na samun kariya.

Hukumar lafiya ta Duniya WHO ta ce wannan na iya sauya fama da ake yi da cutar, sai dai sun kara da cewar akwai bukatar yin amfani da gidajen sauro da kuma maganin kashe kwari.

Maleriya tana kashe fiye da mutum 400,000 a shekara - fiye da rabin wannan adadin kuma yara ne a yankin kudu da Saharan Afirka.

Labarai masu alaka