Birnin Paris ya tsaya cak saboda yajin aiki

Wata mata na yin amfani da na'urar Scooter Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Wasu ma'aikata sun yi dabarar yin amfani da wata kafa domin kaucewa yajin aikin

Jama'a a birnin Paris sun yi cikar kwari a tashoshin jiragen kasan yankin sakamakon yajin aikin da ma'aikatan sufuri suke yi dangane da yunkurin yiwa tsarin fansho garambawul.

An garkame tashoshi 10 cikin 16 sai dai a wasu tashohin harkoki sun fuskanci tazgaro sabanin yadda aka sa ba.

Akasarin ma'aikatan sun yi tattaki wasu sun yi zaman dirshan a gidajensu sai tayin samun abin hawa a kyauta karkashin tsarin samun abin hawa a zamanance.

Yajin aikin, wanda shi ne mafi girma a tarihi tun shekarar 2007, shi ne gangami na farko da aka gudanar domin nuna kin jinin tsarin pensho na gamagari wanda shugaba Macron ya bijiro da shi.

Sabon tsarin fanshon zai maye gurbin tsare-tsaren pensho na ayyuka daban-daban.

Wasu da ga cikin ma'aikata har da lauyoyi da ma'aikatan tashohin jiragen sama da likitoci sun nemi a tsunduma yajin aiki da ga ranar Litinin.

Wane hali ake ciki a Paris?

Hukumomi sun ce akwai wuraren da ke fuskantar cunkoson ababen hawa har na tsawon kilomita 235 a birnin na Paris, fiye da cunkoson da ake samu a baya.

Kafofin yada labarai sun nuna yadda jama'a suka yi dandazo a hudu daga cikin tashoshin jiragen kasa, inda wasu suka niki gari domin yin bulaguro.

Jaridar Le Parisien ta ce ba a kai ga cika ka'idojin bangaren shari'a na samar da daidaito sakamakon yajin aikin da aka gudanar a shekarar 2007 wanda shi ma ya nuna kin jini ga yiwa tsarin fansho garambawul.

Uku da ga cikin tashohin jirgin kasan biyar, karkashin kulawar hukumar da ke sa ido kan ayyukan jiragen kasan, na gudanar da harkokinsu yadda ya kamata sai dai biyu da ga cikin jiragen suna yin tayin rage cunkoson sannan da rashin samun jiragen kasan har zuwa yammacin ranar.

Matafiya sun ce an kara kudin tsarin hawa jirgi na Uber inda wani dan jarida ya wallafa wani hoto da ke nuna kudin hawa Uber kan fam 90 wanda ya ninka kudin da ala sana biya.

Labarai masu alaka