'Yan Najeriya sun yi zarra a gasar karatun Kur'ani a Saudiyya

Wadanda sukja yi nasara a gasar karatun Kur'ani ta 2019 a Saudiyya Hakkin mallakar hoto @makkahregion
Image caption 'Yan Najeriya uku ne suka yi zarra a gasar ta bana

Wasu 'yan Najeriya uku Abubakar Muhammad da Amir Yunus Goro da kuma Abdulganiyyi Amin sun yi nasarar lashe kyautuka a gasar karatun Al Kur'ani ta 2019 a kasar Saudiyya a matakai daba-daban.

Gwamnan garin Makka Khalid Al Faisal ne ya gabatar masu da kyautukan, kamar yadda Makka Region ta wallafa a shafinta na Twitter.

Gwani Idris Abubakar Muhammad daga jihar Borno ta Najeriya, ya zo na daya ne a ajin farko na izu sittin ba tare da tafsiri ba.

Wannan nasara da ya samu ta ba shi damar lashe kyautar riyal na Saudiyya 120,000 - kimanin kusan naira milyan ₦12,000,000.

Sai Amir Yunus, wanda shi kuma ya zo na uku a ajin farko na izu sittin da tafsiri, inda ya samu kyautar riyal 150.000 - sama da naira miliyan ₦14,000,000.

Abdulganiyyi Amin shi ne na ukun, wanda ya zo na uku shi ma a aji na biyu na izu sittin ba tare da tafsiri ba.

Shi kuma ya samu kyautar riyal 40,000 - kusan naira miliyan ₦4,000,000.

Wannan ita ce musabakar al Kur'ani ta Sarki Abdulaziz karo na 41, wadda aka saba gudanarwa a kasar Saudiyya.

Karin labaran da za ku so ku karanta:

Labarai masu alaka