Amurka za ta sanar da sunayen masu hannu a harin 11 ga Satumba

Baraguzan inda aka kai harin 11 ga watan Satumba a birnin New York na Amurka Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Kusan mutane 3000 ne suka mutu a lokacin harin

Ma'aikatar shari'a a Amurka ta ce za ta sanar da sunayen jiga-jigan 'yan Saudiyya da ake zargi da taimakawa maharan da suka kai harin ranar 11 ga watan Satumba a kasar.

Ta ce za a gabatar da duk abin da bincike ya samo ga lauyoyin iyalan wadanda lamarin ya shafa, sai dai kawo yanzu ba a bayyana ko za a fadi sunan mutumin a bainar jama'a ba.

Sha biyar daga cikin mahara sha tara na kungiyar al-Qaeda da suka kai harin 'yan asalin kasar Saudiyya ne.

A shekarar 2004 kwamitin da majalisa ta kafa dan binciken lamarin ya gano babu wata shaida da ta nuna gwamnatin Saudiyya ce ta samar da kungiyar ta al-Qaeda.

Harwayau, a shekarar 2012 wani rahoto na hukumar FBI na bincike akan 'yan Saudiyya Fahad al-Thumairy da Omar Ahmed al-Bayoumi da ake zargi da taimakawa maharan.

Shi dai al-Thumairy tsohon jami'in diflomasiyya ne, ya yin da al-Bayoumi ake kyautata zaton tsohon jami'in hukumar leken asirin Saudiyya ne kamar yadda jaridar Washington Post ta bayyana.

Rahoton na FBI da aka fitar da shi cikin sirri ya ce akwai wani mutumin na daban amma ba a bayyana sunansa ba.

Iyan mutanen sun bukaci a gurfanar da gwamnatin Saudiyya gaban shari'a, kuma suna son a bayyana ainahin sunan mutumin da a iya cewa shi ne kashin baya kuma wanda ya taimakawa maharan cimma manufarsu.

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Mutane 3000 ne suka mutu a mummunan harin da ya girgiza Amurka

A ranar 11 ga watan Satumbar shekarar 2011, maharan suka tuka jirgin da sukai garkuwa da shi tare da dannawa dogon ginin cibiyar kasuwanci ta World trade Centre da ke birnin New York.

Da kuma wani jirgin na daban da mahara suka danna ginin ma'aikatar tsaro ta Pentagon da ke Washington, sai kuma wani jirgin da aka harbo ya fani a wani katon fili da ke Pennsylvania.

Kasar Saudiyya ta dade ta na musanta hannu a kai harin ko taimakawa maharan.

Me ma'aikatar tsaron Amurka ke cewa?

A ranar Alhamis ne ma'aikatar ta ce Attoney General William Barr ne ya bada umarnin kar a bayyana sunan jami'n Saudiyyar.

An bayyana cewa Mista Barr ya dauki matakin kar a bayyana sunan dan sirrin kasa, musamman ga iyalan wadanda lamarin ya shafa.

Amma hukumar FBI ta ce 'yan uwa da iyalan na da hakkin sanin ainahin abin da abin da ya faru tare da kwato musu hakkinsu daga wadanda suka aikata laifin ta hanyar hukuntasu.

A rahoton na shekarar 2012 dai, 'yan uwan da iyalan sun yi hasashen ta yiwu wani babban jami'i ko mai fada aji a Saudiyya ne ya taimakawa maharan, dan haka sun yi na'am da matakin da ma'aikatar shari'a ta dauka.

Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ambatoTerra Strada daya daga cikin wakilan iyalan wadanda lamarin ya shafa na cewa lallai ya zama wajibi a bayyanawa iyalan gaskiyar abinda ya faru. dan su na da hakki kan hakan.

Labarai masu alaka