Harin Saudiyya: Iran ta yi Allah wadai da kalaman Amurka

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
.

Iran ta zargi Amurka da yunkurin tayar da zaune tsaye bayan da Sakataren Harkokin Wajen kasar Mike Pompeo ya ce gwamnatin Iran na da hannu dumu-dumu a harin da aka kaddamar wa wasu matatun mai mallakar Saudiyya guda biyu.

Mista Pompeo yayi watsi da ikirarin 'yan tawayen Houthi na daukar alhakin kai harin, wadanda kuma ake zargin suna samun goyon bayan kasar ta Iran.

Ministan harkokin wajen Iran Javad Zarif ya ce zarge-zargen da ake yi wa kasarsa ba shi ne zai kawo karshen rikicin Yemen ba.

Kasar Saudiyya ta bayyana cewa harin ranar Asabar din da aka kaddamar mata, ya janyo mata tsaiko wajen fitar da gangar mai miliyan 5.7 da ta saba fitarwa a kowacce rana.

Yanzu haka dai idanun kasashen duniya na kan kasuwar hada-hadar man fetur ta duniya da za'a bude ranar Litinin, inda masana ke jiran tsammanin tashin farashin man fetur.

Tun bayan hambarar da gwamnatin tsohon shugaban Yemen a shekara ta 2015, ake kai ruwa rana tsakanin 'yan tawayen Houthi da Saudiyya waccea ke samun goyon bayan kasashen yammaci.

A cewarsu, sun tura motocin yaki guda goma da za su kai hari a wata masana'antar sarrafa mai da ke Khurais a safiyar ranar Asabar.

Amma Mista Pompeo ya ce "babu wata hujjar" da ke nuna cewa motocin yakin sun fito ne daga Yemen, hakan ya sanya ya zargi Iran din da hannu a harin.

Amurka ta kuma zargi Iran da hannu a harin da aka kaddamar wa wasu rijiyoyin mai a yankin a wannan shekarar, a dai-dai lokacin da dangantaka ke kara tsami tsakanin kasashen biyu,

Wannan na zuwa ne biyo bayan matakin Shugaba Donald Trump na kara kakaba wa Iran din takunkumi, lamarin da ya sanya kasar yin watsi da yarjejeniyar kera makaman nukiliya.

Me Iran ta ce game da zargin Amurka?

Ministan harkokin wajen kasar Javad Zarif a shafinsa na Twitter ya ce gazawar Amurka na matsawa kasarsa lamba ya sanya yanzu ta koma shirya labaran kanzon kurege.

Zarif na magana ne kan matakin gwamnatin Amurka na matsin lamba kan Iran din da kuma kakaba mata takunkumi.

Hakkin mallakar hoto NASA

Javad Zarif yace Amurka da kawayenta sun yada zango a Yemen a wani nufi nasu kamar yadda suka ce 'yan tawaye na kokarin durkusar da kasar.

Me ikirarin Mista Pompeo yake nufi?

Sakataren harkokin wajen Amurkan bai bayyana wasu hujjoji da za su tabbatar da zargin da yake yi wa kasar Iran din ba, sai kawai yace "Muna kira ga kasashen duniya da su yi Allah wadai da harin da harin da Iran ta kaddamar."

Amurka da kawayenta za su tabbatar da cewa 'An dauki tsauraran matakai kan Iran sakamakon harin da ta kai", a cewar sa.

A baya Amurka ta zargi Iran din da kai hari kan wasu tankokin mai guda biyu a yankin Gulf tsakanin watan Yuni zuwa Yuli, tare da kai wani harin a watan Mayu.

Tuni gwamnatin Tehran ta yi watsi da zarge-zargen da Amurka da kawayen ke mata kan hare-haren

Idan har 'yan tawayen Houthi suka kwashe tankokin dakon man daga Yemen, za su dauki daruruwan mil kafin su isa inda suke son kaiwa.

Idan aka kwatanta nisan da ke tsakanin iyakar Yemen da matatar mai ta Khurais akwai tazarar kilomita 770, wanda hakan ke nuni da cewa ya zarce harin yau da kullum da mayakan suka saba kai wa.

Wani bincike da Majalisar Dinkin Duniya ta gudanar ya gano wani jirgin yaki marar matuki mallakin mayakan na Houthi, wanda ake ganin ka iya kai hari zuwa nisan kilomita 1,500.

Jaridar Wall Street Journal ta wallafa cewa masana na bincike kan harin da aka kaddamar ko yana da alaka da arewacin kasar- wato ko dai Iran ko kuma abokan kawancen Shi'a da ke Iraki, wajen yin amfani da makamai masu linzami maimakon amfani da jirgi marar matuki wajen kaddamar da harin sama.

A ranar Lahadin da ta gabata, Firai Ministan Iraki Adil Abdul-Mahdi ya musanta "abin da ake yadawa a shafukan sada zumunta cewa an yi amfani da yankinsa wajen kai hari kan matatun mai na Saudiyya da jirage marasa matuka".

Jaridar Washington Post ta ce gwamnatin Amurka ta yi imanin cewa an lalata rukunin gidaje 15 a Abqaiq da ke gefen Yamma da kuma Arewa maso Yamma, baya ga yankin Kudancin kasar.

Labarai masu alaka

Karin bayani