Ko Amurka za ta daukar wa Saudiyya fansa kan Iran?

Satellite image showing attack on Saudi Aramco facility, 15 September 2019. Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Hotunan tauraron dan adam da ke nuni da yadda aka kai wa kamfanin mai na kasar Saudiyya, Saudi Aramco hari

Amurka ta fitar da wasu hotunan tauraron dan adam sannan ta bayyana wasu bayanan sirri da suka samu da ke nuna cewar kasar Iran na da hannu wajen kai hari a kamfanin Saudi Aramco.

Tuni dai kasar Iran ta musanta zargin dangane da harin da 'yan tawayen Houthi na Yemen da ke samun goyon bayan Iran din suka yi ikrarin kai wa.

To sai dai wasu jami'an kasar Amurka da ba a fadi sunansu ba da suka zanta da kafafen watsa labaran kasar da ma na duniya, sun ce bisa la'akari da girman harin ya sa su kokwanton 'yan tawayen Houthi ne suka kai shi.

Sakamakon harin dai ya janyo raguwar danyen mai a duniya da kaso biyar sannan kuma farashin ya yi tashin gwauron zabbi.

Me Amurka ke fadi?

Sakataren harkokin kasashen waje na Amurka, Mike Pompeo ya zargi Iran a karshen mako ba tare da nuna wata kwakkwarar hujja ba, al'amarin da ya tilasta wa Iran bayyana Amurka da mayaudariya.

Da yake bayani a shafinsa na Twitter ranar Lahadi, Shugaba Donald Trump bai fito karara ya zargi kasar Iran da kai harin ba, amma ya nuna yiwuwar daukar matakin soji kan duk wanda aka samu da laifin aikata wannan hari.

Wasu jami'an kasar ta Amurka da ba a bayyana sunansu ba sun zanta da jaridar New York Times da gidan talbijin na ABC da kuma kamfanin dillancin labarai na Reuters.

Wani jami'in ya ce kamfanin na Aramco ya samu matsaloli guda 19 sannan kuma an kai harin ne daga yamma maso arewacin ginin wato ba daga bangaren da 'yan Houthi ke iko da shi ba a Yemen.

Hakan kuwa in ji jami'an na nuna yiwuwar kai harin ne daga yankin Gulf ko kuma daga Iran ko Iraki.

Iraki dai ta musanta yiwuwar kaddamar da harin daga yankunanta.

Tuni dai kasar China ta nemi kasashen da su mayar da wukakensu kube.

Ita ma Birtaniya ta bakin sakataren harkokin wajenta, Dominic Raab ta ce babu takamaiman wanda za a dora wa alhakin kai wannan hari da ya bayyana da 'karya dokokin kasa da kasa".

Me Iran ta ce?

Har yanzu dai Iran ba ta kai ga mayar da martani ba dangane da sabbin batutuwan da Amurka ta yi kan harin.

To sai dai ministan harkokin wajen Iran din, Javad Zarif ya wallafa a Twitter ranar Lahadi inda yake yin shagube ga Mike Pompeo cewa "sakamakon kasa matsa wa Iran lamba sakatare Pompeo ya koma amfani da yaudara".

Javad Zarif yana nuni ne ga batun da gwamnatin Donald Trump ta yi na amfani da 'karfi fiye da kima" wajen kakaba wa Iran jerin takunkumi tun bayan da Amurkar ta fice daga yarjejeniyar nukiliyar Iran.

Yadda aka kai harin

An dai kai harin ne ranar Asabar kan Abqaiq, wurin da shi ne wurin sarrafa danyen mai mafi girma a duniya da kamfanin mai mallakar kasar Saudiyya, Aramco ke kula da shi da kuma rijiyoyin mai da ke Khurais.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption An ta ganin hayaki na ta tashi sama daga Abqaiq

Saudiyya ta ce jirage maras matuka ne suka kai harin da misalin karfe 04:00 agogon Saudiyya, inda hayaki ya turnuke.

'Yan tawayen Houthi sun ce dakarunsu ne suka aike da jiragen maras matuka guda 10 zuwa wuraren kuma tun lokacin sun yi gargadin cewa akwai yiwuwar karin wasu hare-hare.

Ba a samu wasu rahotannin jikkata ba to amma har yanzu ba a iya tantance irin barnar da harin ya yi ga wuraren ba.

Labarai masu alaka