Fargaba ta biyo bayan harin da aka kai wa Saudiyya

Harin sama da rundunar da Saudiyya ke jagoranta ta kai a Dhamar da ke kasar Yemen, ranar 1 ga watan Satumba Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Hare-haren rundunar hadin gwiwar da Saudiyya ke jagoranta kan 'yan tawayen Houthi a Yemen

'Yan tawayen Houthi sun dauki alhakin kai harin; Amurka na zargin Iran na da hannu a ciki; Iran ta nesanta kanta daga harin.

Musayar yawu da aka yi hasashe ta biyo bayan harin da aka kai wa matatar mai mafi muhimmanci ta kasar Saudiyya.

Hare-haren sun nuna irin gagarumin hadarin da ke fuskantar matatun man, masu matukar muhimmanci ga tattalin arzikin duniya.

Kasar Saudiyya - wacce ke da goyon bayan Amurka, wadda kuma sojojin haya na Yammacin Duniya ke tuka jiragen yakinta - ta dade tana kai hare-haren sama a kan 'yan tawayen Houthi.

Amma yanzu 'yan tawayen sun nuna cewa su ma za su iya mayar da martani da kansu.

Babu shakka hare-haren na 'yan Houthin sun sake jawo da ce-ce-ku-ce game da irin taimako da tallafin fasahar da Iran ke ba wa 'yan tawayen.

Hare-haren sun kuma kara kawo fargaba a yankin na tekun Fasha da ke fama da zaman dar-dar.

Hare-haren sun kuma fito da gazawar gwamnatin Trump na Amurka a fili, wajen aiwatar da tsarin amfani da matsanancin karfi a kan Tehran.

Yayin da ake ci gaba da nuna wa juna yatsa a kan hare-haren, akwai wani abu da ba mu da cikakkiyar masaniya a kai.

A baya dai, 'yan tawayen Houthi sun sha amfani da rokoki da jirage marassa matuka wajen kai wa Saudiyya hari.

A baya hare-haren jirage marasa matukan ba su da wani tasiri.

Sai dai kuma dace da nisan zangon hare-haren 'yan tawayen na baya-bayan nan ya sauya tunani a kan yadda aka dauki lamarin.

Tambayar ita ce shin da gaske an yi amfani da jirage marassa matuka a harin, ko kuma dai rokoki ne 'yan tawayen suka harba?

Idan har rokoki 'yan tawayen suka harba, to abin tambaya shi shi ne yadda aka yi shingayen rokoki na Saudiyya ba su yi aikinsu ba?

Shin daga yankunan da ke hannun 'yan Houthin aka harba makaman, ko daga wani wuri?

Shin kungiyoyi da ke mara wa Iran baya a kasar Iraqi na da hannu a harin, ko kuma Iran da kanta ce ke da hannu?

Tuni dai sakataren harkokin waje na Amurka Mike Pompeo ya zargi Tehran da hannu a harin, amma da alamu ya yi hakan ne kafin samun kwakkwarar sheda daga bayanan sirri, kasancewar bai bayar da wata hujja da za a iya tantancewa ba.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Mike Pompeo ya ce Amurka da kawayenta za su tabbata an hukunta Iran

Bayan sa'o'i, majiyoyi daga Amurka na cewa an samu wasu hujjoji 17 a kan hare-haren, da ke nuna cewa an harba makaman ne daga arewa ko arewa-maso yamma da Saudiyya.

Hakan kuma na nuna cewa daga Iran ko Iraqi aka harbo makaman, ba daga Yemen ba wacce ke kudu da Saudiyya.

Amurka ta kuma yi alkawarin ba da karin bayanai a kan hare-haren.

Kasar ta kara da cewa tana yin nazari a kan hare-haren wasu rokoki da jirage marasa matuka da suka kasa isa inda aka harba su.

Iran na da kyakkyawar alaka da 'yan Houthi.

Ana kuma kyautata zaton kasar ta taimaka masu wurin mallakan makamai masu cin dogon zango, ta hanyar amfani da jirage marasa matuka ko rokoki.

A shekarar 2018, rahoton wani kwararre a Majalisar Dinkin Duniya ya ce akwai kamanceceniya sosai tsakanin jirgi maras matuki mai suna Qasef-1 na 'yan Houthi da Ababil-T na kasar Iran.

Binciken ya zargi Iran da karya takunkumin samar da makamai a Yemen, inda ta bai wa 'yan Houthi dabaru da kayan yaki.

A shekarar 2017 ma an gano hakan, bayan nazarin da hukumar da ke bincike kan samar da makamai a rikice-rikice mai zaman kanta ta gudanar, wanda ya mayar da hankali a kan taimakon jirage marasa matuka da Iran ke bayarwa.

Sai dai kuma zangon da Qasef-1/Ababil-T ke ci bai wuce kilomita 100-150 ba.

Amma tazarar da ke tsakanin kan iyakar Yemen da filin hakar mai mafi kusa da ita a Saudiyya Kilomita 770 ne.

Saboda haka idan har da jirage marasa matuka aka kai hare-haren, to akwai yiwuwar an sabunta kirarsu, kuma an kara masu nisan zango da nagarta.

Yanzu akwai yiwuwar su ma 'ya Houthi sun mallaki makamai masu cin dogon zango kamar Iran, amma babu isassun hujjoji da ke tabbatar da cewa an yi amfani da makaman a rikicin Yemen.

Akwai kuma yiwuwar cewa rokoki ne aka harbo daga Iraqi ko Iran, amma cikakkiyar amsar wadannan tambayoyi na bukatar kwararan hujjoji da aka tattaro daga bayanan sirri.

Duk da cewa ba sai an yi bayani filla-filla ba, amma an riga an samu matsala a dangantakar diflomasiyya.

Amurka da Saudiyya na takun saka da Iran.

Kuma gwamnatin Trump ta riga ta cimma matsaya, inda ta zargi Iran da kwace jiragen ruwan wasu kasashe a yankin Gulf.

Iran ta fito fili ta kwace wani jirgin dakon mai mallakin Burtaniya, bayan ita ma an tsare mata jirgin manta a gabar Gibraltar.

Gwamnatin Trump na ganin cewa alamu sun riga sun bayyana cewa Iran ta taimaka wa 'yan Houthi a kai hare-haren da suka kai wa matatutn man Saudiyya.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Saudiyya na kokarin ganin ta ci gaba da hakowa da kuma tace mai bayan hare-haren da aka kai mata

Abin tambaya yanzu shi ne me za su yi, ko kuma me za su iya yi a kai?

Amsar na iya zama: ba wani abin a zo a gani.

Amurka na goyon bayan Saudiyya, duk da cewa ana samun karuwar adawa da rikicin na Yemen a Capitol Hill, fadar gwamnatin kasar, inda ake ganin rashin amfanin hare-haren saman da Saudiyya ke jagoranta, wanda ke kara jefa Yemen din da ke fama da talauci, kara neman agaji.

Akwai kuma wadansu abin damuwa da hare-haren kwanan nan suka kawo.

Duk da goyon bayan da gwamnatin Trump ke wa Saudiyya da kuma barazanar amfani da karfin tuwo, a zahiri babu abin da ke nuna cewa barazanar da Amurkan ke wa Tehran din kaifi daya ne.

Hakkin mallakar hoto NASA
Image caption Hoton tauraron dan'adam da ke nuna hayakin da ya turnike daga harin da aka kai wa matatar mai a Saudiyya

Da alamu Trump na son ya ci gaba da ganawa da Iran kafin taron babban zauren Majalisar Dinkin Duniya da ke tafe.

Kwanan nan, Trump din ya sallami mai ba shi shawara kan harkokin tsaro, Mike Bolton, wanda ke kan gaba wajen neman kawo sauyin gwamnati a Tehran.

Iran da kawayenta 'yan Houthi na amfani da dabarar mai rauni wurin yakar mai karfi, ta hanyar musanta zargi da kuma amfani da sojojin haya ko ba da bayanai ko ta shafukan intanet.

Tehran na sane da kurin Trump da wuyar sha'aninsa, don haka take neman jefa Amurka a cikin wasu sabbin sarkakiyar yunkurin amfani da karfin soji.

Hakan zai bai wa Iran damar ita ma ta yi amfani da karfin da ya wuce misali.

Hadarin shi ne idan aka yi rashin dace, bangarorin na iya shiga yaki, wanda ba a fatan hakan.

Labarai masu alaka