Ina so na fi kowa iya yin siddabaru- Babs Cardini
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Ina so na fi kowa iya yin siddabaru – Babs Cardini

Ku latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon

Ni da rufa-ido Danjuma da Danjummai ne, in ji Babs Cardini, dan Najeriya mai shekara 19.

Ni kaina kamar siddabaru nake. Kuma a duk inda na yi yana burge mutane.

'Yan Najeriya suna yawan roko na in yi masu siddabarun da za su samu kudi.

Na fara sha'awa siddabaru tun ina dan shekara biyar, kuma na fara yin shi a matsayin sana'a a shekara 16.

Nan da shekara uku masu zuwa ina so in zama cikin manyan masu rufa ido a duniya, in ji matashin.

Labarai masu alaka