Har yanzu ni ne Shugaban R-APC – Buba Galadima
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Har yanzu ni ne Shugaban R-APC – Buba Galadima

  • Latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon

Jagoran 'yan jam'iyyar APC da suka ware daga uwar jam'iyyar Injiniya Buba Galadima ya ce har yanzu shi ne shugaban bangaren da ya ware.

Buba Galadima ya bayyana haka lokacin da ya kawo mana ziyara a ofishinmu na Abuja a makon jiya.

Ita dai R-APC, wadda Buba Galadima ke wa jagoranci ta balle ne daga jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya lokacin da aka samu sabanin ra'ayi tsakanin 'ya'yanta.

Bayan kafa R-APC ne wasu jiga-jigan jam'iyyar APC suka sauya sheka zuwa jam'iyyar adawa ta PDP.

Cikin wadanda suka sauya shekar akwai tsohon Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki da Sanata Rabiu Kwankwaso da Gwamnan jihar Benue Samuel Ortom da Gwamnan jihar Sakkwato Aminu Tambuwal da sauransu.

Har ila yau, Buba Galadima yana cikin kwamitin yakin neman zaben Atiku Abubakar wato dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP a babban zaben 2019, wanda Shugaba Muhammadu Buhari ya lashe.

Buba Galadima yana daya daga cikin wadanda suka bayar da shaida a gaban kotun sauraron kararrakin zabe da aka kammala a farkon watan nan.

Kotun ta yi watsi da karar, inda ta jaddada nasarar da Buhari ya samu, kamar yadda tun farko INEC ta bayyana.