Harin matatun mai - Amurka za ta tura sojoji Saudiyya

US Secretary of Defence Mark Esper (L) and Chairman of Joint Chiefs of Staff General Joseph Dunford at a press conference in August 2019 Hakkin mallakar hoto Getty Images

Amurka ta bayyana aniyarta ta tura sojoji Saudiyya a daidai lokacin da kasar ke fuskantar barazanar hare-hare ga matatu da kuma kamfanonin mai na kasar.

Sakataren tsaro na Amurka Mark Esper ya shaida wa manema labarai cewa sojojin da za a tura za su je ne domin tabbatar da tsaro, sai dai bai bayyana adadin dakarun da za a tura ba.

A makon da ya gabata ne dai 'yan tawayen Houthi na kasar Yemen suka dauki alhakin kai hari ga wasu matatun mai biyu na Saudiyyar.

Sai dai Amurka da kuma Saudiyya sun dora alhakin kai harin ga Iran.

A ranar Juma'a ne Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana sabbin takunkumai ga Iran inda kuma ya ce yana so ya guji yaki tsakanin kasashen.

Wannan sabon takunkumin da Mista Trump ya kakabawa Iran din zai fi mayar da hankali ne ga babban bankin Iran din da kuma kadarorinta.

Me shelkwatar tsaron Amurka ke cewa?

Mista Esper ya bayyana cewa Saudiyya da kuma Hadaddiyar Daular Larabawa sun bukaci agaji daga Amurka.

Ya bayyana cewa dakarun Amurka za su fi mayar da hankali wajen kara habaka kariya ga duk wani hari da za a kawo musamman na makamin roka ko mai linzami, hakazalika Amurkar za ta yi kokarin gaggauta kai makamai duka kasashen biyu.

Me ya faru da matatun mai na Saudiyya?

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Abqaiq matatar mai ce mafi girma a duniya

A kwanalkin baya ne dai aka kai wasu hare-hare da jiragen sama masu sarrafa kansu a gabashin kasar.

An dai kai hare-haren ne kan wasu wurare biyu da ake sarrafawa da adana albarkatun man fetur.

Jami'an gwamnatin kasar sun ce gobara ta tashi a sanadiyyar hare-haren musamman a matatar mai ta Abqaiq - wacce ita ce irinta mafi girma a duniya - da kuma a Khurais, inda ake hako mai.

Kafofin watsa labarai na Saudiyyar sun ce an shawo kan gobarar da ke ci. Tun farko, hotunan bidiyo da aka wallafa a shafukan sada zumunta sun nuna yadda gobarar ta haska samaniya a Abqaiq.

A wasu bidiyon, ana iya jin karar harbe-harbe a bayan fage, tamkar ana gwabza fada.

Duk da cewa 'yan tawayen Houthi na Yemen sun dauki alhakin kai harin, Saudiyya da Amurka sun dage kan cewa lallai Iran ce ta kai harin

Labarai masu alaka