Harajin Banki: Babban Bankin Najeriya ya zama dan fashi – Gudaji
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Cajin kudin ajiya zai hana ajiya a banki - Gudaji

Dan majalisar tarayya Gudaji Kazaure ya yi Allah-wadai da harajin ajiyar kudade da Babban Bankin Najeriya (CBN) ya yi.

Ya bayyana cewa hakan zai sa mutane su daina kai kudadensu banki, wanda hakan zai iya sa 'yan fashi su rika kwace kudade a hannun mutane wanda hakan zai kawo rudani a cikin kasa.

Dan majalisar ya ce ba za su bari dokar ta tsaya ba domin za ta tsawwala wa jama'a a lokacin da kudi ke wahalar samu:

"Abin ya yi mani ciwo. Abin da ya sa ya yi mani ciwo, shi ne kudi suna wahalar samu a kasar nan."

Labarai masu alaka