Tsige Trump: Masu kwarmato za su shiga tsaka mai wuya

Trump speaks at a Hispanic Heritage month event Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption An zargi shuagan Amurka da matsin lamba ga kasashe masu karfi don wani buri na kashin kansa

Lauyoyin wani dan fallasa wanda korafin da ya yi ya janyo yukurin tsige shugaban Amurka sun ce kalaman shugaba Donald Trump sun jefa rayuwar mutumin da suke karewa cikin hadari.

Tun bayan da aka bayyana tattaunawarsa da shugaban kasar Ukraine ne, Mr Trump ya yi kira da a bayyana wanda ya fallasa batun.

'Yan jam'iyyar Democrat sun ce wanda ya kwarmata bayanan zai bayar da shaida a gaban majalisa "nan ba da dadewa ba" da zarar an dauki matakan kare yadda za a san ko shi wane ne.

Mista Trump ya ce za a iya kama makiyansa da laifin "cin amanr kasa".

Wata takarda mai dauke da tattaunawar Trump da sabon shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ta nuna cewa shugaban Amurka ya nemi takwaransa na Ukraine da ya yi bincike kan wasu zarge-zargen cin hanci da rashawa marasa tushe da aka yi wa tsohon mataimakin shugaban kasa kuma dan takarar shugabancin Amurkar a zaben 2020, Joe Biden da kuma dansa.

Wannan ne ya janyo yunkurin da 'yan jam'iyyar ta Democrat su ke yi na neman tsige Mr Trump daga mukaminsa, amma cimma hakan na bukatar 'yan jam'iyyar Republican su juya wa shugaban baya.

A ranar Lahadin da ta wuce ne shugaban kwamitin tattara bayanan sirri na jam'iyyar Democrat, Adam Schiff, ya ce majalisa ta kusa kammala shirye-shiryen na ganin mai kwarmaton ya bayar da shaida a asirce.

Ko me fallasar ya ce?

Wasikar wadda ta fito daga tawagar lauyoyin mai fallasar - wadda kuma a cikinta ake jan hanklai kan kalaman Mista Trump - an tura ta ne ga mukaddashin hukumar tattara bayanan sirri ta kasa, Joseph Maguire, a ranar Asabar kuma ta fito bainar jama'a ranar Lahadi.

Lauyansa Andrew Bakaj ya rubuta cewa "abubuwan da suka faru a 'yan makonnin da suka wuce sun kara janyo damuwa ga wanda muke karewa cewa za a bayyana wa jama'a su san ko shi wanene, kuma idan hakan ta faru to za a jefa rayuwarsa cikin hadari."

Wasikar ta fito karara ta bayyana kiran da shugaba Trump ya yi a makon jiya cewa a bayyana wanda ya yi fallasar da kuma wanda ya bashi bayanan tattaunawar.

Wasikar ta ambato Mista Trump na cewa: "Ina so in san wanda ya baiwa mai kwarmaton wadannan bayanan, don wanda ya bayar da bayanan ya yi kama da dan leken asiri.

"Kun san abin da muke yi a sanda muke da wayo? game da dan leken asiri da kuma cin amanar kasa? To a yanzu mun dan sauya yadda muke yi da su."

Haka kuma wasikar ta yi nuni da wata kyautar dalar Amurka dubu 50 da wasu 'yan gani kashenin Trump suka yi alkawarin bayarwa ga duk wanda ke da bayanan da za su kai ga gane wanda ya yi kwarmato.

"A tsammaninmu wannan yanayi zai kara tabarbarewa tare da kara jefa mutumin da muke karewa dama wasu masu kwarmaton cikin gagarumin hatsari, yayin da majalisa ke aiwatar da bincike kan wannan lamari.

Me shugaba Trump ya ce?

A ranar Lahadi da yamma ne Mr Trump ya sake wallafa wani gargadin da wani bako a shirin Fox News ya yi a shafin Twitter na cewa idan aka tsige shugaban kasar hakan zai janyo "yakin basasa da zai zamo tamkar karayar ce ga kasar nan wadda ba za mu taba warke wa ba".

Dan majalisa mai wakiltar Illinois na jam'iyyar Republican, Adam Kinzinger ya yi tur da sakon da Trump ya aika da cewa "abin kyama ne".

"Ina so na hadu da ba ma wanda ke zargina kadai ba... har ma da mutumin da ya mika bayanai ba a hukumce ba, wanda kuma galibin maganar ma ba haka ta ke ba, ga mai 'fallasar'.' shin wannan mutumin na LEKEN ASIRI ne a kan shugaban kasar Amurka? Babban abu zai biyo baya!"

A ranar Litinin kuma shugaban ya ci gaba da kamfe din nuna adawar ga mai kwarmaton da kuma dan majalisa Schiff a shafinsa na Twitter.

Inda ya rubuta cewa "Ina so a yi wa Schiff kwararan tambayoyi kan cin hanci da kuma cin amanar kasa."

A karshen mako ne 'yan Republican suka fara kamfe din kare shugaba Trump, amma da alamun wasu jiga-jigan jami'ar jam'iyyar sun yi tur da abin kunya baya-bayan nan da shugaban kasar ya yi.

Tom Bossert, tsohon mai baiwa shugaban kasar shwara kan harkokin cikin gida ya gaya wa ABC News cewa: " kiran da shugaban ya yi ya dame ni matuka, har ma dukkan abin da ke faruwa."

Haka kuma ya yi tur da Mista Trump wajen yada "abin da aka riga aka musanta" cewa kasar Rasha ba ta da hannu wajen satar bayanan sakonin emails na 'yan Democrat a yayin zaben 2016, duk kuwa da cewa hukumar tattara bayana sirrri ta kasa ta ce an yi hakan.

Labarai masu alaka