Koriya ta Arewa ta yi gwajin makami mai linzami daga teku

Koriya ta Arewa ta tabbatar da cewa ta yi gwajin wani sabon makami mai linzami, wanda babban ci gaba ne daga gwaji na matsakaicin zango da ta yi tun watan Mayu.
Makamin wanda ke iya daukar makamin kare dangi, shi ne na 11 da Koriyar ta yi gwajinsa a wannan shekarar.
Amma shi wannan wanda aka harba daga teku, za a iya harba shi daga jirgi mai iya shiga can kasan teku.
Samun sundukin mai shiga kasan ruwa na da muhimmanci domin yana nufin Koriya ta Arewa za ta iya harba makami mai linzami nesa daga kasarta.
- Me ya sa aka sake kama Abdurrashid Maina?
- "Mun sha bakar wuya a makarantar kangararru ta Kaduna"
- Adam Zango ya 'yi wa malamin da ya yi masa 'kazafi' Allah-ya-isa'
A cewar wani jami'in kasar Koriya ta Kudu, makamin ya yi tafiyar nisan kilomita 450 kafin ya sauka cikin ruwa.
Wannan na nufin makamin ya ninka nisan tashar binciken sararin samaniya ta duniya duk da cewa a baya Koriya ta kudu ta harba makamin da ya fi wannan nisa.
Makamin ya fada ne a cikin tekun Japan, wanda Koriya ta Kudu ke kira da "Tekun Gabas". Japan ta ce ya fada ne a kusa da tsibiri da ke da nisan kilomita 200 kusa da iyakarta.
Gwajin ya zo ne sa'o'i kadan bayan da Koriya ta Arewa ta bayyana cewa za ta ci gaba da tattauna wa da Amurka.