Ali Nuhu ya taya Adam Zango murna

Fati Washa Hakkin mallakar hoto Instagram
Image caption Fati Washa ta nuna murnar zagayowar samun 'yancin Najeriya da hotuna a shafinta na Instagram

Allah ya kawo mu Juma'atu babbar rana, ranar da ke alamta hutun karshen mako mai dimbin farin jini.

Wannan makon ya zamo mai muhimmanci a Najeriya don a ranar Talata ne kasar ta cika shekara 59 da samun 'yanci daga turawan mulkin mallaka.

Masu iya magana dai kan ce rai dangin goro ne, sai da ban iska.

Tunda mako ya zo karshe, an yi ta fadi tashi da kai-komo, bari mu dan kutsa shafukan sada zumunta mu lalubo wainar da aka toya a duniyar fina-finan Hausa don mu nishadantu.

Jaruma Fati Washa ta wallafa hotuna da dama a shafinta na Instagram a wannan makon amma wanda ya fi daukar hankali shi ne wani hoto da ta wallafa ranar 1 ga watan Oktoba, wato ranar da Najeriya ta cika shekara 59.

Fati ta sanya koriyar rigar 'yan kwallo da farin mayafi mai alamar tutar Najeriya kuma ta daga kanta sama tana dariya.

Wannan hoton ya janyo ce-ce-ku-ce inda wasu suka rika sukar yanayin shiga suna ganin cewa surar jikinta ta bayyana.

Wata mai amfani da shafin mai suna @alimikeh ta ce "Gaskiya wannan rigar ba ta dace ba duk surar kirjinki ya bayyana."

Yayin da @b.simoli ya ce "Adai tuna cewa akwai MUTUWA."

Wasu masu amfani da shafin na Instagram kuwa sun bar wa jarumar sakonni na kambamawa da yabo a karkashin hoton.

Jarumi Ali Nuhu ya wallafa hotuna kala-kala a shafinsa na Instagram amma wanda ya fi daukar hankali shi ne hoton jarumi Adam A Zango da ya wallafa yana yi masa murnar zagayowar ranar haihuwarsa.

Hoton ya samu 'like' sama da 18,000.

Haka kuma, Ali Nuhu ya sa hotunansa kala 3 ranar 1 ga watan Oktoba sanye da koriyar taguwa da farin wando rike da tutar Najeriya.

Jaruma Rahama Sadau ta yi wata sanarwa a shafukanta na Twitter da Instagram sai dai ta bar masu bibiyarta a cikin duhu.

Jarumar ta wallafa wani hoto mai dauke da rubutun "Sadauz Home" kuma ta ce tana farin ciki da wannan sanarwa, sai dai fa ba ta bayyana abin da take sanarwar ba.

Ta bukaci masu bibiyarta su canki manufar wannan kuma wanda ya canka dai-dai za ta ba shi goron gayyatar bude wani wuri.

Sama da mutane dari da hamsin ne suka yi ta yin tinini-tanana a karkashin wannan sako na Rahama a shafin Twitter, don canko gaskiyar lamarin da kuma yin nasarar lashe kyautar jarumar.

Kawo yanzu dai jarumar ba ta fayyace abin da hoton ke nufi ba.

Jarumi Adam Zango, wanda a yanzu ya nisanta kansa daga Kannywood ya zuba hotuna da bidiyo a shafinsa na Instagram wanda suka hada da bidiyon wakokinsa da fina-finansa da yake saki a shafin Youtube.

Sai dai wani hoto da ya ja hankali shi ne wani wanda ya hada hotunan wasu jarumai mata tara a wuri daya kuma a kasansa ya rubuta "Kowa ya ga zabuwa...ku nuna min wadda kuka fi so a cikin jarumaina. Jaruman kamfanina na da da na yanzu."

Jaruman da ke cikin hoton dai sun hada da shaharrarun 'yan wasa kamar su Zainab Indomie da Zainab Umar (Raga) da Fati Ladan da dai sauransu.

Wannan hoto da Zango ya sa ya janyo 'comment' sama da dubu biyu sannan an yi masa 'like' sama da dubu goma.

Adam Zango ya kara da cewa duk jarumar da ta fi yawan masoya 'comments section' zai ba ta kyautar waya samfurin Techno Phantom 9 da katin layin MTN na 20,000 da kwalin Indomie .

Duk wani ma'abocin shafin Instagram kuma mai bibiyar jaruman Kannywood ya san da zaman jaruma Saratu Gidado Daso, don kuwa tana daya daga cikin jaruman da ke nishadantar da masoyanta a shafin.

A wannan makon, Daso ta sa wani hoto na ita da wata tsohuwar jarumar fina-finan Nollywood wato Hilda Dokubo.

Duk wani ma'abocin fina-finan Nollywood a shekarun 1990 zai san Hilda wacce ta kan taka rawar uwargida da kan fada halin kaka-ni-ka-yi.

Haka kuma jarumar ta sa wani bidiyo wanda ke nuna ta tana wasan kwaikwayo a dandali da harshen turanci tare da wasu 'yan wasan na Nollywood.

Mawaki Ali Isa Jita ya fitar da sabuwar waka a wannan makon mai taken 'Arewa Angel'.

Wakar dai ta soyayya ce kamar sauran wakokin Jita kuma jaruma Rahama Sadau ta fito a matsayin matarsa a wakar.

Bidiyon wakar ya samu 'like' sama da dubu goma sha biyar a shafin Instagram kuma jarumai da sauran masoyan Ali Jita suna ta 'repost' a kan wakar.

Wakar Arewa Angel dai ta dauki salon wakokin turanci da 'yan kudu ko turawa kan yi.

Labarai masu alaka