Abba Gida-Gida ya sha kaye a kotu, Buhari ya tafi Afirka ta Kudu: Hotunan Najeriya cikin makon nan

Image caption Wannan shi ne ginin makarantar Daru Imam Ahmad Bun Hambal da ke Kaduna inda hukumomi suka kubutar da daruruwan mutane da ake zargin an azabtar da su. An kwashe kwanaki labarin yana jan hankalin duniya. Ranar Lahadi muka wallafa wannan hoto a ci gaban labarin.
Hakkin mallakar hoto NIGERIA PRESIDENCY
Image caption Ranar Talata aka yi bikin cikar Najeriya shekara 59 da samun 'yancin kai daga Turawan mulkin mallakar Birtaniya. Wannan hoton wasu daga cikin sojojin kasar ne suke faretin ban-girma a fadar shugaban Najeriya da ke Abuja domin tunawa da zagayowar ranar samun mulkin-kan
Hakkin mallakar hoto NIGERIA PRESIDENCY
Image caption Ranar Laraba Shugaba Muhammadu Buhari ya kama hanyar tafiya Afirka ta Kudu tare da wasu gwamnonin kasar, ciki har da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jihar Kano da Gwamna Simon Lalong, wadanda kotunan sauraren kararrakin zabe suka amince da nasarar da suka yi a zaben watan Maris na 2019...
Image caption Sai dai ko da yake hukuncin bai yi wa jam'iyyar PDP dadi ba kuma tuni ta sha alwashin daukaka kara, amma a wannan hoton shugaban jam'iyyar APC na Kano, Abdullahi Abbas(hagu) da kuma na PDP, Rabi'u Sulaiman Bichi sun sha hannu a wajen kotun.
Hakkin mallakar hoto Daily Trust
Image caption Ranar Laraba, hukumomi a birnin Ogbomoso na jihar Oyo suka bayar da labarin mutuwar kunkuru mafi tsawon shekaru a duniya mai suna Alagba. An ce kafin mutuwarsa, kunkurun, wanda ke da shekara 344, yana iya magance larurori.
Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ranar Alhamis, Shugaba Buhari ya shaida wa takwaransa na Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa cewa bai ji dadin hare-haren kin-jinin-baki da 'yan kasarsa suka kai wa wasu 'yan nahiyar Afirka, cikin har da 'yan Najeriya, kwanakin baya ba.
Hakkin mallakar hoto Twitter/@ngrcommtech
Image caption Sarkin Nguru da ke jihar Yobe, mai martaba Alhaji Mustapha Ibn Mai Kyari (hagu) ya kai ziyara ga ministan sadarwa, Isa Ali Pantami a ofishinsa da ke Abuja ranar Juma'a.