Ana samun karuwar bidiyon bogi mai kamar gaske

Getty Images Hakkin mallakar hoto Getty Images

Sabon binciken da aka gudanar ya bayyana cewa ana samun karuwa matuka a bidiyon bogi da ake hadawa wadanda ke wuyar tantancewa, yawan irin wannan bidiyon ya ninka sau biyu a watanni tara da suka wuce.

Akwai hujjoji da ke nuna cewa hada irin wadannan bidiyoyin ya zama babbar sana'a.

Duk da cewa wannan bincike ya fi karkata ne kan yadda ake amfani da irin wadannan bidiyoyi wajen siyasa, hujjoji sun tabbatar da cewa an fi yin irin wadannan bidiyoyin wajen fina-finan batsa.

Kamfanin ''Deeptrace'' ne ya gudanar da wannan bincike wanda kamfani ne da ya shahara wajen samar da tsaro a intanet. Bincikenta ya gano bidiyo kusan 14,698 idan aka hada da Disambar 2018 da aka samu 7,964.

A cikin irin wadannan bidiyoyi an gano cewa wadanda aka yi wa sharri 'yan wasan kwaikwayo ne na Amurka da Birtaniya, haka zalika binciken ya gano harda wasu mawaka na kasar Korea su ma an yi musu irin wannan sharri.

Rahoton binciken ya bayyana amfani da irin wadannan bidiyoyin wajen kamfe din siyasa, amma a lamura kusan biyu da binciken ya nuna - na kasar Gabon da Malasiya, zarge-zargen da ake yi na bidiyoyin bogi an gano ba gaskiya bane.

Amma babban abin a yanzu shi ne, yadda mutane ke hada fina-finan batsa da fuskokin mutane domin cimma wata manufa ko kuma ramuwar gayya.

Hotunan bogi, samun kudi

Kasancewar kamfanin Deeptrace wanda ya gudanar da wannan bincike, wata hujja ce da ke nuna yadda irin wadannan bidiyoyi na bogi suka zama abin damuwa matuka ga gwamnatoci da kuma kamfanoni.

Kamfanin ya bayyana manufarsa a matsayin ''kare mutane da kamfanoni daga irin abubuwan da kan musu illa ta intanet,''

An fara amfani da kalmar ''deepfake,'' a 2017, wacce kalma ce da ke nuni da matukar yadda ake hada bidiyo ko hotuna na bogi, kuma wannan rahoton ya yi bayani kan cewa a cikin shekaru biyu, wannan lamari ya zama babbar sana'a da take kawo wasu manyan kudade.

Binciken ya gano cewa wasu shafukan intanet hudu na batsa da ke kan gaba wajen wallafa irin wadannan bidiyoyi na bogi sun samu kusan mutum miliyan 134 sun ziyarci shafin domin kallo tun Fabrairun 2018.

Irin manhajojin da ake amfani domin hada irin wadannan bidiyoyi sun fara yawa.

Labarai masu alaka