Jami'ar Legas ta dakatar da malami na biyu kan 'neman mata'

Dr Samuel Oladipo Hakkin mallakar hoto Facebook
Image caption Samuel Oladipo

Jami'ar Legas ta sake dakatar da wani malamin na jami'ar sakamakon binciken kwakwaf da BBC Africa Eye ta yi, inda aka nuna yadda ake cin zarafin mata dalibai a jami'o'i biyu da suka yi fice a Afirka ta yamma.

An nuna Dr Samuel Oladipo a binciken yana kokarin ribatar 'yar jaridar da ta yi shigar burtu a zuwan mai neman shiga jami'ar.

Dr Samuel ne mutum na hudu kuma na karshe da jami'ar ta kora tun bayan tona asirinsu da binciken kwakwaf din na BBC ya yi.

Wannan sanarwar dai na zuwa ne bayan da jami'ar Ghana ta ce za ta dakatar da malaman jami'ar guda biyu da aka gani a cikin binciken na BBC suna kokarin neman wadanda suka baddakama a zuwan dalibai.

Malaman guda uku dai Dr Oladipo da Prof Ransford Gyampo da kuma Dr Paul Kwame Butakor sun musanta zarge-zargen da jami'ar ke yi musu.

Da ma dai a ranar Litinin ne jami'ar Legas ta sanar da dakatar da Dr Boniface Igbeneghu, wanda shi ma ya fito a cikin binciken.

Kazalika, Cocin Foursquare Gospel Church, ya dakatar da Dokta Boniface Igbeneghu bayan da aka bankado abin da yake yi a cikin wani shiri na BBC Africa Eye da aka fitar a jiya Litinin.

Hakan ya faru ne bayan bulla rahoton sashen binciken kwakwaf na BBC wato Africa Eye da muka kawo a jiya litinin, kan yadda malamai ke lalata da dalibai dan ba su makin jarabawa ko gurbin karatu.

Shirin BBC Africa Eye da ya bankado yadda malaman jami'a ke lalata da dalibai 'yan mata ya ja hankulan jama'a a shafukan sada zumunta matuka.

Musamman ma bidiyon da ya nuna wani malamin jami'ar Legas Dokta Igheneghu na neman yin lalata da wata 'yar jarida da ta yi shigar 'mai neman gurbin karatu a jami'ar da yake aiki.

Cocin Foursquare Gospel church shi ne wurin ibada da malamin jami'ar ke rike da mukamin fasto, kuma cocin bai yi wata-wata ba ya dakatar da shi daga halartar dukkan ayyukan cocin.

A wata sanarwa, cocin ya ce bai amince da irin halayyar Dokta Igheneghu da mutane ire-irensa ke nunawa ba, kuma cocin ya nisanta kansa daga ta'asar da malamin ya aikata.

Rahoton na BBC wani bangare ne na wani bincike da aka shafe shekara guda ana gudanar da shi kan yadda malaman jami'a ke cin zarafin daliban da aka damka musu amana a jami'o'in Legas da na Ghana.

Jami'ar Legas ma ta nisanta kanta daga halayyar ta malamin, kuma ta ce za ta kori dukkan malamin da aka samu da hannu shi ma yana irin wannan aika-aikar.

Kazalika, Jami'ar Ghana ta musanta cewa tana kokarin rufa wa wasu ma'aikatanta ko dalibai da aka samu da hannu dumu-dumu a wannan abin kunyan, kuma ta ce za ta binciki wadanda aka ambata a cikin rahoton na BBC.

Me yasa aka dakatar da shi?

Bidiyon binciken ya nuna malamin yana yi wa 'yar jaridar BBC wacce ta yi badda kama tambayoyi da kuma neman bukatun da basu dace ba.

A haduwarsu ta karshe, an nadi bidiyon malamin jami'ar na neman cin zarafinta inda yake neman ta sumbace shi cikin ofishinsa.

Ya kuma yi mata barazanar cewa idan ba ta yi masa biyayya ba zai kai kararta wajen mahaifiyarta.

Akwai wasu dalibai a cikin bidiyon da suka zargi malamin da cin zarafin dalibai. Daya daga cikin tsoffin daliban Dakta Igbeneghu wacce aka boye sunanta ta yi zargin cewa malamin ya sa ta so ta kashe kanta so da dama.

A martanin jami'ar Legas kan lamarin, ta yi taron gaggawa kan lamarin a ranar Litinin inda nan take ta dakatar da Dakta Igbeneghu daga aiki kuma ta dakatar da zuwansa cikin makarantar baki daya.

A wata sanarwa, jami'ar ta bayyana cewa ''wannan abin kunya ne matuka'' kan zarge-zargen da ake yi masa kuma ta sha alwashin yin duk abin da ya dace wajen bicike domin yaki da irin wannan matsalar da malamai ke cin zarafin dalibai ta hanyar nemansu da lalata.

Jami'ar ta kuma bayyana cewa ta rufe wani wurin shakatawar malamai da ake kira ''cold room'' wanda a bidiyon an nuna dakin a matsayin wurin da ake zargi malaman jami'a na kai dalibai domin yin lalata da su.

Kazalika, Cocin Foursquare Gospel Church, wacce Dakta Boniface fasto ne a cocin ta nisantar da kanta daga wannan lamari a wata sanarwa da ta fitar.

Sun bayyana cewa cocin ba ta daukar mugayen dabi'u daga fastocinta inda suka bukaci da ya sauka daga mukaminsa.

Sai me kuma bidiyon ya nuna?

Bidiyon binciken kwakwaf din mai tsawon kusan sa'a daya ya nuna harda wasu malaman Ghana biyu.

Dukkaninsu wato Farfesa Ransford Gyampo da kuma Farfesa Paul Kwame Butakor sun musanta cewa suna cin zarafin dalibai ta hanyar jima'i domin basu maki.

Farfesa Gyampo ya shaida wa 'yan jaridan kasar Ghana cewa zai kai BBC kara kotu.

Image caption Hoton ofishin Dakta Boniface bayan an rufe shi a ranar Talata

Jami'ar Ghana ta bayyana cewa za ta yi bincike kan wadanda aka kira sunansu a rahoton kuma jami'ar ta musanta zargin kare ma'aikatanta wadanda suka ci zarafin dalibai.

Me mutane ke cewa dangane da wannan binciken?

Binciken da BBC ta gudanar kan cin zarafin dalibai musamman mata a jami'o'i ya tayar da kura matuka musamman a shafukan sada zumunta.

Masu amfani da shafin Twitter da dama sun yi watsi ko kuma sun nuna rashin jin dadinsu dangane da abubuwan da suka gani a bidiyon, hakan ya jawo wasu dayawa da suka yi shiru a baya suka fito suna kwarmata irin halin da suka shiga makamancin haka da suna jami'a.

Yar' jaridar BBC Kiki Mordi wacce ita ce ta gudanar da binciken kuma ta nadi bidiyon, ta bayyana irin halin da ta shiga a lokacin tana jami'a wanda hakan ya ja dole ta bar tsangayar karatun aikin likitanci ta koma wata tsangayar.

Wata 'yar Najeriya wacce ta kammala jami'a ta shaida wa shirin ''Newsday'' na BBC cewa binciken ya razana ta. ''Ko kafin na shiga jami'a na ji labarin mutumin - ina da kawaye wadanda ya ci zarafinsu.''

Ta bayyana cewa ko kafin ta kammala jami'a sai da ta dauki lokaci kafin ta kai masa kundin bincike na kammala makaranta.

Labarai masu alaka