Kun san kayyyakin da ba za a sanya wa haraji ba a Najeriya?

Buhari Hakkin mallakar hoto Getty Images

Shugaba Muhammadu Buhari na Najerya, ya ce gwamnatinsa ta gina kasafin ne a kan kudin harajin kaya da ake kira VAT, a saboda haka za ta kara yawan harajin daga kaso 5 zuwa 7.5.

Shugaba Buhari ya ce " Dokar ta harajin na VAT ta tsame magunguna da kayan koyo da karantarwa da kayan more rayuwa....."

"Sashe na 46 da dokar kudi ta 2019 ta fadada kayayyakin da karin na VAT ba zai hau kansu ba da suka hada da:

 • Biredi fari ko ruwan kasa
 • Masara da shinkafa da alkama da gero da dawa
 • Kifi da danginsa;
 • Fulawa da abinci mai sitati;
 • Kayan marmari da abubuwa masu kwanso da ganyaye
 • Doya da gwaza da dankalin gida da na turawa
 • Nama da kwai
 • Madara;
 • Gishiri da kayan kamshi
 • Ruwa."

Hakan dai zai bai wa gwamnati damar cike gibin fiye da naira tiriliyan biyu da ke kasafin kudin kasar da aka gabatar ranar Talatar nan.

Buhari wanda ya gabatar da daftarin kasafin kudin a gaban zauren majalisar dokokin kasar, ya ce kasafin na 2020 ya dara na 2019 da kaso 9.7 cikin dari.

Kasafin na 2019 dai ya kai naira tiriliyan 8.83, inda na 2020 zai kama fiye da naira tiriliyan 10.

An gina kasafin na 2020 ne a kan farashin gangar danyen mai dala 57, inda kuma ake hasashen Najeriyar za ta rinka fitar da gangar man 1.86 a kullum.

Kasafi ga ma'aikatu da sassan gwamnati

 • Majalisar dokoki - naira biliyan 125
 • Ma'aikatar Shari'a - naira biliyan 110
 • Aiki da gidaje - naira biliyan 262
 • Sufuri - naira biliyan 123
 • Hukumar ilmin matakin farko ta UBEC - naira biliyan 112
 • Tsaro - naira biliyan 100
 • Aikin gona - naira biliyan 83
 • Albarkatun ruwa - naira niliyan 82
 • Ilimi - naira biliyan 48
 • Lafiya - naira biliyan 46
 • Hukumar Raya Arewa maso gabas - naira biliyan 38
 • Birnin tarayya - naira biliyan 28
 • Neja Delta - naira biliyan 24
 • Ma'aikatar wutar lantarki - naira biliya 127
 • Shirin gina yankunan kasa - naira biliyan 100
 • Masana'antu da zuba jari - naira biliyan 40
 • Ma'aikatar cikin gida - naira biliyan 35
 • Shirin tallafin ga 'yan kasa na Social Investment Programmes - naira biliyan 30
Hakkin mallakar hoto Twitter/@BashirAhmaad

Sabanin lokacin gabatar da kasafin 2019 lokacin da aka yi wa shugaba Buhari ihu a zauren majalisar, a wannan karon 'yan majalisar na ta yi wa shigaban sowar 'Sai Baba'.

Hakan dai wata manuniya ce ga irin zaman lafiya da aiki tare tsakanin bangarorin biyu.

Da ma dai Shugaban masu rinjaye na majalisar wakilai, Alhassan Ado Doguwa, ya shaida wa BBC cewa wannan ne karon farko da shugaban kasar zai gabatar da daftarin kasafin kudi a kan lokaci saboda alakar da ke tsakanin majalisa da bangaren zartarwa.

Ya kara da cewa bangaren zartarwa ya sanya bangaren dokoki a cikin sha'anin kasafin kudin tun ma kafin shugaban ya je zauren majalisar.

A cewarsa, shugaban ya amince a sanya kudin yi wa mazabu aiki (constituency projects) a kasafin kudin 2020, yana mai cewa ba za a samu matsala wurin amincewa da kasafin kudin a wannan karon ba.

Latsa alamar lasifika da ke sama domin sauraren hira da Alhassana Ado Doguwa

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Hirar BBC da Alhassan Ado Doguwa kan kasafin kudin 2020