Yadda alkalan gasar Hikayata ke zaben labaran da suka yi zarra
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Bidiyon yadda ake zabar labaran Hikayata ta 2019 suka yi zarra

Latsa hoton da ke sama don kallon bidiyon:

Alkalan Gasar Rubutun Gajerun Labarai ta Mata ta BBC Hausa, wato Hikayata, suN fara aikin fitar da labarai uku da suka ciri tuta a bana a yau Talata.

Daga cikin wadannan labarai uku ne kuma za a zabi labarin da zai hau matsayi na daya a gasar.

"Wani muhimmin bambanci tsakanin gasar bana da ta baya", a cewar mukaddashin Shugaban Sashen Hausa na BBC, Aliyu Abdullahi Tanko, "shi ne a bana sai ranar da za a karrama gwarzuwar gasar za a fadi sunan wacce ta yi nasara.

"Domin haka ko wacce daga cikin marubutan da labarin ta ya kai wannan mataki za ta iya kasancewa Gwarzuwar Gasar".

Wannan ce shekara ta hudu ta gasar, kuma a cewar Malam Aliyu Tanko, shiga gasar da mata suka yi daga sassa daban-daban na duniya na "nuna yadda iyayenmu mata ke da shaukin yin rubutu da ma shiga wannan gasa."Baya ga labarai ukun da alkalan za su zaba, za su kuma fitar da wasu 12 wadanda suka cancanci yabo.

A bara dai Safiyya Jibrin Abubakar ce ta lashe gasar da labarinta mai suna "'Ya Mace", wanda ya yi shagube a kan halin da 'ya'ya mata kan fada a tsakanin al'umma.

Labarai masu alaka