'Turkiyya ta fara kai wa Kurdawa harin sama a Syria

Turkish army Hakkin mallakar hoto AFP

Jiragen yakin sama na Turkiyya sun kai harin bama-bamai a wasu sassan arewa maso gabashin Syria a yunkurinta na fatattakar mayakan Kurdawa daga yankin.

Shugaban Turkiyya, Recep Tayyip Erdogan ya ce suna kai hare-haren ne da manufar korar Kurdawa sannan a samar da wani sansani wanda za ta tsugunar da 'yan gudun hijrar Syria miliyan 3.6 da suka tsallaka Turkiyya.

An dai ce harin ya janyo mutuwar fararen hula in ji mayakan na Kurdawa.

Sojojin kasa na Turkiyyar har wa yau na maci a kan iyakar ta Syria inda suke jiran umarni suka afka.

Shugaba Donald Trump na Amurka ya janye dakarun kasarsa daga yankin, al'amarin da ya janyo masa suka a ciki da wajen kasar.

Ya kuma kare janye dakarun da ya yi a ranar Talata, inda ya ce ba wai sun kware wa Kurdawa baya ba ne, inda ya bayyana su da 'mutane na musamman'.

Kurdawa dai sun kasance kawayen Amurka wajen samun nasara kan kungiyar IS a Syria.

To sai dai Turkiyya na daukar dakarun Kurdawan da suka mamaye rundunar hadin gwiwa ta Amurka a Syria wato US-allied Syrian Democratic Forces (SDF) a zuwan kungiyar 'yan ta'adda.

Ana dai ganin janye dakarun Amurka daga yankin tamkar bai wa kasar Turkiyya dama ta far wa dakarun Kurdawan ne.

Hakkin mallakar hoto Getty Images

A ranar Talata ne dai Turkiyya ta bayyana cewa a shirye take ta fara yakin da ta dade tana shiryawa a arewa maso yammacin Syria, inda za ta kai hari ga mayakan Kurdawa wadanda kawayen Amurka ne.

Wannan sanarwar ta zo ne bayan Shugaba Trump ya bayar da umarnin janye mayakan Amurka daga iyakar kasar, wanda hakan ya jawo ake ta sukar wannan yunkurin na shugaban.

Mista Trump ya sake kare wannan yunkurin nasa a ranar Talata inda ya bayyana cewa ba wai ya yanke hulda da Kurdawa bane.

A wasu jerin sakonni da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Mista Trump din ya bayyana Turkiyya a matsayin abokiyar kasuwanci da kuma kawa ga kungiyar tsaro ta Nato.

Hakan kuma ya zo ne sa'o'i kadan bayan ya ce zai lalata tattalin arzikin Turkiyyar idan kasar ta wuce ka'ida.

A martanin da Turkiyyar ta mayar dangane da kalaman Mista Trump, mataimakin Shugaban Turkiyya Fuat Oktay ya ce kasar ba za ta bada kai bori ya hau ba idan dai kan batun shirin da take yi ne na yaki a arewa-maso yammacin Syria.

A ranar Talata, Fadar White House ta tabbatar da cewa Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan zai kai ziyara Amurka ranar 13 ga watan Nuwamba bisa gayyatar da Mista Trump ya yi masa.

Me Turkiyya za ta yi a Syria?

A taron babban zauren Majalisar Dinkin Duniya na baya-bayan nan, Shugaba Erdogan ya gabatar da taswirar wani yanki mai fadin kilomita 480 da ba a yaki a iyakar Syria da yake so kasarsa ta kula da shi.

Yankin zai zama matsuguni ga 'yan Syria kimanin miliyan 3.6 da ke zaman gudun hijira a Turkiyya.

A ranar Litinin ma'aikatar tsaron Turkiyya ta ce "an kammala dukkanin shirye-shirye domin daukar matakin," kuma kafa irin wannan yankin na da "muhimmanci" ga 'yan Syria da kuma samar da aminci a yankin.

Sai dai Turkiyya ta sha yin barazanar kai hari a kan mayakan Kurdawa a iyakokin Arewa-maso-yammacin Syria.

Turkiyya na daukar 'yan sa kan Kurdawa na YPG a matsayin wani reshe na haramtacciyar kungiyar Kurdawa da ta kwashe shekara 30 tana neman ballewa daga Turkiyya.

A wani bangare kuma a ranar Talata Iran ta bayyyana adawarta da duk wani matakin soji da Turkiyya za ta dauka a Syria.

Mayakan SDF na gudanar da wasu sansanonin 'yan gudun hijira da na rike iyalen wadanda ake zargin mayakan kunigyar IS ne a ciki da wajen yanki mai amincin da Turkiyya ke bukata.

Ana rike da iyalen wadanda ake zargi mayakan IS a Ain Issa da Roj da ke cikin yankin.

Sansani mafi girma shi ne na Al-hol, da ke kusa da iyakar Iraki, kuma yake da nisan kilomita 60 daga Tukiya. Mutane 70,000 ne ke sansanin Al-hol, kashi 90 dinsu mata da kananan yara ne, wadanda suka hada da mutum 11,000 'yan kasashen ketare.

Labarai masu alaka