An jefe dan sanda har lahira a Malawi

'Yan sanda a Malawi Hakkin mallakar hoto AFP

'Yan sanda a Malawi sun bayyana sunan wani jami'insu da aka kashe ranar Talata yayin taho mu gama da masu zanga-zangar nuna kin jinin gwamnati a Msundwe- wani yanki a yammacin babban birnin kasar, Lilongwe.

Kakakin rundunar 'yan sandan James Kadadzerab ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa an jefe dan sanda mai suna Usumani Imedi har lahira.

Yana cikin 'yan sandan da ya tunkari masu zanga-zangar da suka rufe babbar hanyar da ke Msundwe, inda ke da yawan 'yan hamayya, don hana magoya bayan Shugaba Peter Mutharika halartar taron siyasarsa na farko a birnin, tun bayan nasarar da ya yi a zaben watan mayu mai cike da ce-ce-ku-ce.

Masu goyon bayan bangaren hamayya sun fusata da yadda hukumar zabe ta gudanar da zaben, inda suka yi zargin an yi magudi.

Ministan tsaron cikin gida Nicholas Dausi ya ce masu bin titin sun bukaci 'yan sanda su kawo dauki bayan da masu zanga-zangar suka rufe titin.

"Da 'yan sanda suka iso, sai suka fara jifar su har ta kai mun rasa jami'inmu daya".

'Yan sanda sun harba hayaki mai sa hawaye don tarwatsa zanga-zangar amma sai masu yin ta "suka ci gaba da taruwa kuma suka rika jefa duwatsu, har suka tare dan sanda daya a lungu suka jefe shi har lahira," kamar yadda wani shaida ya bayyana wa AFP.

A kalla mutum 12 aka kama kuma ana san ran za a sake kama wasu, in ji jaridar Nation ta kasar.

Shugaba Mutharika ya gudanar da taron daga baya a babban birnin kasar kuma ya bukaci a zauna lafiya a kasar, inda ya ce: "Wannan kasarmu ce. Kada mu kona ta."

Labarai masu alaka