Bidiyo: Yadda tankokin yakin Turkiyya ke kokarin shiga Syria

Na'urarku na da matsalar sauraren sauti
Yadda tankokin yakin Turkiyya ke kusantar iyakar Syria

Turkiyya ta kara yawan dakarunta da ke kan iyakar Syria a wani yunkurin kutsawa da take shirin yi domin far wa mayakan Kurdawa da dakarun Amurka ke jagoranta.

Dakarun na Syria za su ketara zuwa Syria nan ba da jimawa ba, in ji wani mai tamaka wa shugaba Erdogan.

Turkiyya na son kafa sansani wanda za ta tsugunar da 'yan gudun hijrar Syria miliyan 3.6 da suka tsallaka Turkiyya, bayan kuma ta fatattaki mayakan na Kurdawa.

Shugaba Donald Trump na Amurka ya janye dakarun kasarsa daga yankin, al'amarin da ya janyo masa suka a ciki da wajen kasar.

Labarai masu alaka