Bincike: Mata a Najeriya na shiga tasku a lokacin haihuwa

The Lancet

Sabon rahoton ya ce kaso daya bisa uku na mata a kasashe matalauta na Afirka da Asia sun fuskanci tursasawa lokacin haihuwa.

Rahoton ya ce wasu daga cikin matan sun sha mari da baa da sauran nau'in cin zarafi yayin da suke gadon haihuwa a asibitoci.

Nazarin wanda aka buga shi a jaridar lafiya ta The Lancet ranar Laraba, ya ce mata a kasashe kamar Najeria da Myanmar da Ghana da kuma Guinea na yawan fuskantar tiyata da kuma yin kari yayin haihuwa ba tare da amincewarsu ba inda kuma mafi yawancin lokuta ba tare da yin amfani da magungunan dausashe ciwo ba.

Sabon nazarin da Hukumar Lafiya ta Duniya ta jagoranta ya bi mata fiye da 2000 da ke nakuda, inda aka ji ra'ayin matan fiye da 1,600 bayan sun haihu.

Kaso 42 sun ce an zage su da cin zarafi a lokacin da suke kan gwiwa. Wasu matan sun ce an dake su ko yi musu tsawa ko kuma an daddanne su da karfin tsiya.

Har wa yau, daga cikin matan 2,016 da nazarin ya sanya wa ido lokacin haihuwa, kaso 13 daga cikin tiyatar da aka yi musu da kuma kaso 75 na karin da aka yi musu an yi musu ne ba tare da amincewarsu ba.

Rahoton ya kara da cewa a cikin kaso 59 na duba al'aurar mata masu ciki ana yi ne ba tare da yardarsu ba.

Kaso 57 na mata 2,672 da aka tattauna da su sun ce ba a ba su maganin dausashe ciwo ba lokacin da ake yi musu tiyata.

Bugu da kari, rahoton ya ce asibitoci kan hana matan tafiya gidajensu bayan sun haihu saboda ba su biya kudin magani da zaman asibitin ba.

Daga karshe nazarin ya nemi da a kyale mata su zabi wanda suke son ya zauna tare da su a lokacin haihuwa da kuma yi musu abubuwa bisa amincewarsu sannan a gyara dakunan karbar haihuwa domin tsare mutuncin matan.