Jirgin Iran ya fashe a gabar tekun Saudiyya

Amjad na daga cikin cikin jiragen daukar danyen mai biyu da aka lalata a wasu hare-hare masu sarkakiya a 2019 Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Amjad na daga cikin cikin jiragen daukar danyen mai biyu da aka lalata a wasu hare-hare masu sarkakiya a 2019

Rahotanni daga Iran sun ce wani jirgin dankon man Iran din ya yi bindiga bayan tashin wani abin fashewa a kusa a gabar tekun Saudiyya da ke Jiddah.

Kafofin yada labaran Iran sun ce fashewar jirgin ta auku ne a tazarar kilomita 97 daga gabar.

Gobarar ta lalata manyan rumbunan mai biyu na jirgin ruwan mallakin kamfanin mai na kasar Iran (NIOC) da kuma tsiyayar mai a tekun Maliya.

Zuwa yanzu babu karin bayani kan ko akwai hasarar rayuka a gobarar jirgin mai suna Sabiti, kamar yadda kamfanin NIOC ya bayyana.

Wata kafar talabijin din Iran Al Alam ta ce an harbi jirgin ne da makamai masu linzami, amma kamfanin jiragen dakon mai na Iran (NITC) ya karyata zargin.

Kamfanin NITC ya ya ce an yi nasarar kashe gobarar da kuma tsayar da malalar man, yayin da hukumomin Iran ke bincike domin gano musabbabin lamarin.

Wata majiya daga cibiyar nazarin harkokin jiragen ruwa ta Windward ta sheda wa BBC cewa irin wadannan jiragen sun saba kashe na'urorinsu na tantancewa (AIS), domin kar a gane inda suke - yawanci domin kauce wa hukunci ko matsin lamba daga Saudiyya.

A bisa doka, wajibi ne jiragen su kunna AIS dinsu a kusa da mashigar ruwa ta Suez.

Amma majiyar ta Winward ta ce Sabiti ya nuna wasu bakin dabi'u.

Majiyar ta ce Sabiti ya kunna AIS dinsa tun daga daruruwan kilomitoci kafin isowarsa Suez, alhali jirgin ya buya na tsawon wata biyu.

Lamarin na zuwa ne yayin da ake tayar da jijiyoyin wuya tsakanin Iran da Saudiyyya.

A watan jiya ne aka kai wa cibiyoyin man Saudiyya hari da jirage sama marasa matuka 18 da rokoki bakwai.

Saudiyya na zargin Iran ce ta kai harin.

Jami'an Amurka na zargin Iran da kai wa wasu jiragen dakon mai biyu hari a tekun Gulf a cikin watannin Yuni da Yuli, baya ga harin da Iran din ta kai wa wasu jirage biyu a watan Mayu.

Iran ta musanta zargin hannunta a cikin lamarin.

Labarai masu alaka