Martanin da ya biyo bayan binciken BBC na lalata da mata a jami'a
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Martanin da ya biyo bayan binciken BBC na lalata a jami'a

Duniya na yin martani kan binciken lalata da mata da wasu malaman jami'a ke yi domin ba su makin jarabawa.

Mutane a kasashen Ghana da Najeriya na ci gaba da Allah-wadai da lamarin tare da kira ga mahukunta da su kawo karshen mummunar ta'adar.

Sashen binciken kwakwaf na BBC Africa Eye ne ya gudanar da binciken, inda aka tura 'yar jarida wacce ta badda-kama a matsayin daliba 'yar shekara 17.

Malaman jami'a biyu ne aka nuna a bidiyon binciken, wadanda tuni jami'o'in nasu suka dakatar da su.