Za mu rage 'yan Somalia daga Amurka - Donald Trump

Donald Trump

Shugaban Amurka, Donald Trump ya fada wa magoya baya a yayin wani gangami a Minneapolis cewa zai dauki tsauraran matakai kan sake tsugunar da 'yan gudun hijrar kasar Somalia da ke neman mafaka a jihar Minnesota.

Jihar ta Minnesota dai ta kasance wadda tafi yawan 'yan gudun hijrar na Somalia a duk fadin Amurka.

Donald Trump ya tuna wa magoya bayan nasa dangane da kokarinsa na rage tsugunar da 'yan gudun hijra a Amurka da kaso 85 tun bayan kama aiki.

Shugaba Trump ya ce "Shekaru da dama shugabannin Amurka sun kawo 'yan gudun hijra masu dimbin yawa daga Somalia zuwa jiharku ba tare da lura da abin da hakan zai haifar ba akan makarantu da al'ummomi da kuma masu biyan haraji.

"Na yi alkawari cewa zan bai wa jama'a dama dangane da tsare-tsaren da suka shafi 'yan gudun hijra sannan zan sanya tsauraran matakai wajen tantance 'yan gudun hijrar."

Shugaba Donald Trump bai kyale 'yar majalisar nan 'yar asalin kasar Somalia, Ilhan Omar wadda take wakiltar yankin da ake Mista Trump yake yin gangamin, inda har ya bayyana ta da 'Abin kunya'.