Hukuncin kisa ga masu auren jinsi a Uganda

Launin kalar da masu auren jinsi suke amfani da ita
Image caption Launin kalar da masu auren jinsi suke amfani da ita

Uganda na shirin ayyana hukuncin kisa ga masu auren jinsi a kasar,

Ministan kula da kyawawan dabi'u Simon Lokodo ya sanar da aniyarsa ta sake dawo da dokar haramta auren jinsi wadda baya kotun tsarin mulkin kasar ta soke a 2014.

Simon Lokodo ya sheda wa Reuters cewa idan kudurin ya zama doka za a rika yanke hukuncin kisa ga duka wadanda aka kama da laifin auren jinsi a kasar.

"Dokokinmu na yanzu na da rauni. Dokokin sun haramta auren jinsi ne kawai. Muna so ne a bayyana karara cewa duk wanda aka samu yana ko da tallatawa ne ko daukar masu auren jinsi aiki ya aikata babban laifi. Su kuma masu yin auren jinsin, za a yanke masu hukuncin kisa."

Ministan ya kara da cewa "auren jinsi ya saba wa dabi'ar mutanen Uganda". Ya ce 'yan luwadi na kara daukar hayar mutane "a makarantu inda suke gangamin tallata "karerayin cewa haka aka halittaci mutane a matsayin 'yan luwadi".

A watan Fabrairun 2014, shugaba Yuweri Museveni ya rattaba hannu a kan kudurin dokar - mai suna dokar "A Kashe 'Yan Luwadi" - domin tsananta hukunci a kan 'yan luwadi.

Daga baya a watan Augusta kotun kundin tsarin mulkin kasar ta soke kokar a matsayin haramtacciya, bisa hujjar cewa majalisar kasar ta mayar da kudurin ya zama doka ba tare adadi mafi karancin na 'yan majalisar da ake bukata sun halarci zaman ba.

Mista Lokodo ya ce sabuwar dokar wadda za a sake gabatar wa majalisar a makonni masu zuwa ta samu goyon daga Museveni da 'yan majalisa.

Ministan ya sheda wa wani gidan talabijin na kasar cewa yana da kwarin gwiwan samun goyon bayan kashi biyu cikin ukun 'yan majalisar.

"Muna tattaunawa da 'yan majalisa kuma mun samu goyon bayan akasarinsu ...yawancinsu sun bayyana amincewarsu."

Image caption Mista Lokodo

Shekara biyar da suka gabata kasashen yammacin duniya, ciki har da Amurka, sun dakatar da bayar da takardun biza da tallafi sannan suka soke atisayen soji a Uganda.

Amma Mista Lokodo ya ce a shirye Uganda take a kowane irin mummunan matakin da za a dauka a kan sabuwar dokar.

"Ba ma son bita da kulli," inji shi.

"Muna sane cewa masu ba mu tallafi ta fuskar kudade da gwamanti ba za su ji dadin hakan ba, amma ba za mu mika wuya ba ga masu neman tursasa mana wata bakuwar al'ada."

A dokar kasar ta yanzu - wadda ta samo asali tun lokacin mulkin mallakan turawan Ingilishi - akwai hukuncin dauri ga masu luwadi da madigo. Masu rajin kare hakki na ganin sabuwar dokar za ta ba da damar kai farmaki ga masu auren jinsin.

Fafaroma Julian Onziema daga cikin gamayyar kungiyoyin 'yan luwadi da madigo a Uganda ya sheda wa Reuters cewa 'yan kungiyar na cikin fargaba.

"A baya da aka gabatar da dokar, ta haifar da manyan laifuka masu alaka da kyamar 'yan luwadi da madigo," inji shi.

"An tirsasa wa daruruwan 'yan luwadi da madigo gudun hijira daga Uganda, kuma karin wasu za su tafi gudun hijira da zarar an aiwatar da sabuwar dokar. Wannan dokar za ta haramta mana neman hakkokin 'yan luwadi da madigo, ballantana ta ba su kariya."

Mistsa Onziema ya ce an kashe wasu 'yan luwadi uku da wata 'yar madigo a hare-haren kyama a Uganda a wannan shekara.

Na karshe shi ne wanda aka bankade wani dan luwadi ya mutu a makon jiya.

Labarai masu alaka