Ana yunkurin dandake masu fyade a Jihar Ekiti

Kayode Fayemi Hakkin mallakar hoto Getty Images

Jihar Ekiti dake kudancin Najeriya na yunkurin yi wa dokokin jihar da suka danganci jinsi gyaran fuska da manufar fito da hakuncin yin dandaka ga mutanen da aka kama da laifin yi wa mata fyade da masu lalata.

Tuni dai wasu mata a jihar suka fara yin yabo ga shirin na gwamnati, inda suka ce illar da masu fyade da lalata yara ke yi ta fi dandakar da ake kokarin tanadar musu.

Matan sun ce dandake mutanen da aka kama da laifin fyade zai taimaka wajen rage matsalar fyaden.

Ana ci gaba da yin kiraye-kiraye ga gwamnati da ta tabbatar masu fyade ba su tsira ba.

Matan sun bukaci iyaye su koya wa 'ya'yansu ilimin jima'i, domin su fahimci take-taken masu neman lalata da su.

To sai dai wani masanin halayyar dan-Adam, Dr. Dare Adelusi, ya ce yi wa masu fyade dandaka ba shi ne mafita ba wajen dakile faruwar fyade.

Ya kara da cewa abin da ya kamata a yi shi ne gano dalilin da ya sa masu fyaden ke aikata hakan, ta yadda za a san hanyar hana su.