Aubameyang da Jurgen Klopp sun karbi kambun Satumba

Pierre-Emerick Aubameyang Hakkin mallakar hoto Getty Images

An sanar da sunan dan wasan Arsenal, Pierre-Emerick Aubameyang a matsayin dan kwallon Premier na watan Satumba.

Dan wasan mai shekara 30 ya ci kwallaye biyar a wasanni hudu na gasar da suka hada da kwallon da ya ci Aston Villa a wani bugun tazara.

An kuma sake ayyana kocin Liverpool, Jurgen Klopp a matsayin kocin da ya fi kowanne a watan na Satumba.

Liverpool dai ta zama gagara-badau bayan casa Newcastle United da Chelsea da Sheffield United a watan Satumba.

Jurgen Klopp ya buge kocin Bournemouth, Eddie Howe da na Chelsea, Frank Lampard da kuma na Leicester City, Brendan Rodgers.

Pierre-Emerick Aubameyang wanda dan asalin kasar Gabon ne ya buge Trent Alexander-Arnold da Kevin de Bruyne da Son Heung-min da kuma Riyad Mahrez, a samun wannan kambun.