Abiy Ahmed ya lashe kyautar Nobel

Firai Minista Abiy Ahmed Hakkin mallakar hoto Getty Images

Firai ministan Ethiopia Abiy Ahmed ya yi nasarar lashe kyautar Nobel ta zaman lafiya.

Shugaban ya sha yabo bayan da ya sa hannu kan wata yarjejeniyar zaman lafiya da Eritrea bara, bayan kwashe tsawon shekaru ashirin ana takaddama.

Ofishin Firai ministan ya fitar da sanarwa wacce take kunshe da sakonnin farin ciki da cewa yana alfahari da wannan babbar kyauta.

Ofishin ya ce tun hawansa mulki a bara, "ya mayar da hankali wajen tabbatar da zaman lafiya da yafiya".

Shugabannin kasashe da hukumomin duniya na ci gaba da mika sakon murna ga Shugaba Abiy Ahmed bayan sanarwar ba shi kyautar.

Shugaban hukumar agaji ta Majalisar Dinkin duniya ya ce Abiy Ahmed ya cancanci wannan kyauta.

Shi ma kansa Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Gueterres ya ce "tsare-tsaren Abiy Ahmed sun taimaka wa Ethiopia da Eritrea wajen kafa tarihin dawo da zaman lafiya":

Shugabannin kasashen Liberia da Somalia duk sun bayyana farin cikinsu da samun wannan kyauta.

Abiy Ahmed dai ya yi wa dubban fursunonin siyasa afuwa, sannan ya bai wa kungiyoyin hamayya da 'yan jarida damar yin ayyukansu bayan kwashe shekaru ana tauye masu hakki.

Kokarinsa na kawo karshen rikicin siyasa a Sudan ya taimaka wajen daukar matakin ba shi wannan kyauta ta Nobel.

Amma wasu sun soki wannan matakin, saboda kamar yadda kwamitin Nobel din ya ce, har yanzu akwai matsalolin da ba a magance ba a Ethiopia.

Labarai masu alaka