'Yan Syria 100,000 sun yi hijira saboda hare-hare

Residents flee their home town of Ras al-Ain Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Residents flee their home town of Ras al-Ain

Akalla mutane 100,000 ne suka yi kaura daga gidajensu a arewacin Syria sakamakon hare-haren Turkiyya a yankunan da ke hannun mayakan Kurdawa.

Rahotannin Majalisar Dinkin Duniya sun ce mutanen na zama ne a makarantu da wasu gine-gine da garuruwan lHassakeh da Tal Tamer.

Turkiyya ta fara kai hare-hare a Syria ne a ranar Laraba bayan shugaban Amurka Donald Trump ya janye dakarunsa daga yankunan.

Hukumomin agaji sun tabbatar da mutuwar farar hula 11, tare da hasashen adadin zai karu.

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Yara 'yan gudun hijira a yankin Hasakeh da ke Arewa-maso-yammacin Syria.

Gomman mayakan Kurdawa - karkashin rundunar SDF da mayakan sa kai masu goyon bayan Turkiyya ne aka kashe. Rundunar sojin Turkiyya ta tabbbatar da mutuwar jami'inta daya.

Masana na ganin janyewar dakarun Amurka ya ba wa Turkiyya damar fara kai hari zuwa cikin Syria.

Yawancin yankin da Turkiyya ka kai hare-hare ya fice daga ikon gwamnatin Syria ne sakamanon yakin basasan kasar da aka fara a 2011. Mayakan SDF ne ke iko da yankin tun a 2015.

SDF na daga cikin manyan kawayen Amurka a yakin da take yi da kungiyar IS. Amma Turkiyya na ganin mayakan SDF din a matsayin 'yan ta'adda' da ke goyon bayan masu tayar da kayar baya a Turkiyya.

Me ke faruwa a yakin?

Ranar Alhamis, Turkiya ta kusa yi wa garuruwan Ras al-Ain da Tal Abyad da ke kan iyaka kawanya.

Turkiyya na cewa matakin da ta dauka na samun biyan bukata, amma majiyoyin Kurdawa da kungiyar sa ido kan keta hakkoki ta Syrian Observatory for Human Rights (SOHR) sun ce harin bai yi wani tasiri ba.

Amurka ta aike da karin dubban sojoji saboda barazanar Iran

Kungiyar agaji ta Kurdish Red Crescent ta ce an kashe farar hula 11, yayin da wasu 28 suka samu munanan raunuka, yawancinsu yara ne a ya garuruwan Ras al-Ain Qamishli da ke kan iyaka.

Akalla mutum biyar, cikinsu har da jarirai ne aka kashe a hare-haren da mayakan Kurdawan suka kai a garuruwan da ke kan iyakan Turkiyya.

SOHR ta ce akalla mayakan SDF 29 da 'yan sa kan Syria masu goyon bayan Turkiyya 17 ne aka kashe, yayin da dakarun Turkiyya suka kwace kauyuka akalla goma, a cewar rundunar sojin Syira.

Mutanen da suka yi kaura fa?

Kalubalen gudun hijira na karuwa yankin. Ofisihin 'yan gudun hijira na Majalisar Dinkin Duniya ya ce mutanen da lamarin ya tilasta musu yin kaura daga muhallensu ya kai 100,000, amma kungiyoyin agaji sun ce adadin zai kai 450,000.

Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Residents flee their home town of Ras al-Ain

Ma'aikatan agaji na cewa galibin farar hular da ke garin Tal Abyad sun yi hijira, yayin da wadanda suka rage ke cikin zaman dar-dar.

Ofisihin ya ce hare-haren sun lalata ababen more rayuwa irinsu tashoshin ruwan sha. Dubban mutane na iya rasa tsaftataccen ruwan a yankin Hasakeh, inji rahoton ofishin.

Turkiyya na nema kafa wani 'yanki mai aminci' mai fadin kilomita 480 a kan iyakarta ta bangaren Syria, sai dai ta ce matakin sojin da ta dauka ba zau wuci nisan kilomita 32 ba.

Your contact details
Disclaimer

Karin bayani