Amurka ta aike da karin dubban sojoji saboda barazanar Iran

US Marine Hakkin mallakar hoto AFP

Ma'aikatar tsaro ta Pentagon ta sanar da aikewa da karin dubban sojojin Amurka domin "Kara karfin kariya ga Saudiyya".

Sakataren Tsaro na Amurkar, Mark Esper ya ce ya amince da aikewa da karin dakaru da suka hada da jiragen yaki da kuma na'u'rorin kariya.

Ya ce hakan martani ne ga "irin barazanar da yankin ke fuskanta", a dai-dai lokacin da ake rubanya kokarin kare masarautar daga "hare-haren Iran".

Wannan dai na zuwa ne bayan da aka kai har kan matatun man kasar Saudiyya a watan Satumba.

Yanzu haka dai Amurka ta kara dakaru 14,000 a yankin gabas ta tsakiya tun watan Mayu, kamar yadda gidan talbijin na CNN ya rawaito.

Tun dai lokacin da aka kai wa matatun man Saudiyya harin jirgi maras matuki, al'amarin da ya lalata su, ake ta zargin kasar Iran da hannu.

Tuni dai Iran ta musanta kai harin.

Su ma shugabannin kasashen France da Jamus da Burtaniya sun ce babu wata kwakkwarar sheda cewa Iran din ce ta kai harin.

Karin bayani