Shirin Facebook na bullo da kudin intanet ya samu koma-baya

Facebook ya ce yana fatan kaddamar da kudin na Libra a shekara ta 2020 Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Facebook ya ce yana fatan kaddamar da kudin na Libra a shekara ta 2020

Kamfanin Facebook ya kara samun koma-baya a shirinsa na samar da kudin intanet da ya ce za a rika amfani da shi a duniya gaba daya, mai suna Libra.

Bayan da a makon da ya gabata kamfanin cinikayya ta intanet Paypal ya fice daga shirin, yanzu kuma wasu manyan kamfanonin, Mastercard da Visa da ebay da kuma Stripe dukkanninsu sun bi sahu inda suka fice daga tsarin.

Daman dai hukumomi masu sanya ido a harkar sun nuna shakku ko damuwa kan tsaro da kuma dorewar tattalin arzikin duniya a dangane da shirin na Facebook.

Bisa ga dukkanin alamu wannan shiri na Facebook mai cike da buri, na samar da sabon kudin intanet na duniya, ya kama hanyar wargajewa.

A ranar Litinin ne gamayyar kamfanoni 28, da ke lakabin sunan kudin na Facebook, Libra Association, wadanda suka kirkiri wannan shiri , gamayyar da Facebook din ya kafa domin tafiyar da shirin za ta gana a Geneva.

Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Mark Zuckerberg ya ce zai yi iya iyawarsa wajen hana kamfanin Facebook wargajewa

To amma a yanzu da wadannan manyan kamfanoni biyar masu cinikayya ta intanet suka janye daga shirin, ba a san su waye da su waye za su halarci wannan taro ba.

A dangane da haka munafur da Facebook ya sanar ta bullo da wannan kudi na intanet, mai lakabin Libra, a shekarar da ke tafe, ta shiga wani yanayi na rashin tabbas.

A wata sanarwa gamayyar kamfanonin, wato Libra Association ta ce daman tana sa ran irin mambobin da ta kunsa ya sauya zuwa wani lokaci, amma dai wani abu daya shi ne ko ya hadakar ta kasance shirin zai jure duk wani kalubale, ba tare da ya rushe ba.

Hukumomi musamman a Amurka, sun nuna fargaba da damuwa a kan kudin na intanet na Facebook, Libra, ciki har da hadari ko yuwuwar amfani da shi wurin halatta kudaden haram.

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Kokarin sa mutumin da ya kirkiro Facebook, Mark Zuckerberg ya sauka daga mukamin shugaban kamfanin ya ci tura

A kan hakan ne ma nan gaba a wannan wata na Oktoba, ranar 23, shugaban kamfanin na Facebook, Mark Zuckerberg zai bayyana a gaban kwamitin harkokin kudade na majalisar dokokin Amurka domin amsa tambayoyi game da shirin bullo da kudin da kuma damuwar da ake nunawa game da shirin na kirkiro kudin na intanet, Libra.