Amurka za ta kara tura tulin sojoji Saudiyya

AFP Hakkin mallakar hoto AFP

Shelkwatar tsaron Amurka ta Pentagon ta bayyana aniyar kasar ta tura wasu dubban sojoji Saudiyya domin kara tallafa wa kasar tsaurara tsaro sakamakon ''barazanar'' Iran.

Sakataren harkokin tsaron kasar Mark Esper ya bayyana cewa ya bayar da umarnin tura wasu dakarun da kuma jiragen yaki da manyan makaman kariya.

Ya ce wannan ya biyo bayan barazanar da ake yi wa yankin, kuma duk cikin yunkurin abin da ya kira ''barazanar Iran.''

Wannan yunkurin dai ya zo ne bayan harin da aka kai wa matatun mai na Saudiyya a watan Satumba.

''Idan aka hada da sauran sojojin da aka tura wasu wuraren, jimlar ta kai dakaru dubu 3 kenan da aka amince da tura su cikin watan da ya gabata,'' inji mai magana da yawun shelkwatar tsaron kasar wato Jonathan Hoffman.

Amurkar ta kara yawan sojojin da ta tura yankin zuwa dubu 14 tun watan Mayun bana, kamar yadda kafar watsa labarai ta CNN ta bayyana.

Mista Esper ya shaida cewa Yariman Saudiyya mai jiran gado Mohammed bin Salman ya bukaci taimako daga wajen Amurka.

Harin da aka kai ga matatun mai na Saudiyya ya janyo an samu gibi na kusan kashi biyar cikin 100 na mai da ake samarwa a duniya wanda hakan ya ja aka samu hauhawar farashin mai a kasuwar duniya.

Ko a kwanakin baya sai dai Mohammed bin Salman ya bukaci kasashen duniya da su tashi tsaye wajen daukar mataki dangane da Iran, inda ya bayyana cewa idan ba a yi hakan ba lallai kasar za ta rinka barazana ga duniya.''

Sai dai Iran ta musanta zargin da ake yi mata na kai harin.

Ko a ranar Juma'a sai da Mista Esper ya nananta cewa hujjojin da aka tattara daga hare-haren baya-bayan nan sun nuna Iran din ce ta kai wannan harin.

Labarai masu alaka