Rikicin Tibi da Jikun: An yi zaman sulhu

DARIUS ISHAKU/FACEBOOK Hakkin mallakar hoto DARIUS ISHAKU/FACEBOOK

An yi wani gangami na gamayyar kungiyoyin arewacin Najeriya a jihar Taraba domin samar da sulhu tsakanin kabilun Tibi da Jikun.

Rikici tsakanin kabilun biyu ya ki ci ya ki cinyewa, kuma an dade ana irin wannan zama domin samar da sulhu amma abin ya ci tura.

Gammayar kungiyoyin da ake kira ''Coaltion of Northern Groups'' ta fara ne da hada matasan kabilu biyu ta hanyar hada su kan teburi guda domin tattaunawa irin ta fahimta a Jalingo babban birnin jihar Taraba wanda hakan ya kai ga har sun cimma wata yarjejeniyar zaman lafiya.

Alhaji Ashiru Sherrif, shi ne shugaban kwamitin amintattu na gamayyar kungiyoyin arewacin Najeriyar inda ya bayyana cewa ''mun yarda gaba dayanmu wannan fada ba shi da amfani a cikin al'umma.''

Ya bayyana cewa wannan rikici ya jawo an halaka mutanen da ya kamata a ce nan gaba su ke rike da kasa. Ya kuma shaida cewa a karshe sun dauki matsayi, inda duka kabilun biyu sun amince da a kira manya-manyan shugabanninsu na addini da sarakuna a zauna domin tabbatar da an samu maslaha ta karshe da za a kawo karshen wannan rikici.

A nasa bangaren Mista Daniel Emmanuel Angwi wanda shi ne mai magana da yawun matasa jukunawa a jihar Taraba ya shaida wa BBC gamsuwarsu da bayanan da kungiyoyin suka yi kuma ya nuna rashin jin dadinsa kan yadda ire-iren wadannan abubuwan ke faruwa.

Shi ma a nasa bangaren, Chief Goodman Dahida wanda shi ne shugaban kungiyar walwala da raya al'adun kabilar Tiv a jihar Taraba ya bayyana cewa ya ji dadi matuka dangane da wannan zaman sulhu inda ya ce sun fahimci kurakurensu.

A Najeriyar dai, ana fama da rikicin kabilanci da na addini a wasu jihohi da ke arewacin kasar ciki har da jihar Taraba.

Ko a kwanakin baya sai da gwamnatin tarayyar kasar ta shirya irin wannan zaman sulhu a birnin Abuja inda ta gayyaci manyan masu ruwa da tsaki na kabilun domin kawo karshen rikici tsakaninsu.