Ghana: Mata Musulmai na zanga-zanga kan hijabi

Mata masu zanga-zanga a kasar Ghana ranar 12 ga watan Oktoban 2019 Hakkin mallakar hoto @jabdulai
Image caption Tattakin ya fi tasiri a biranen Tamale da Kumasi da kuma Accra babban birnin kasar

Mata Musulmai a kasar Ghana suna yin zanga-zangar lumana domin bayyana rashin jin dadinsu ga wariyar da suka ce ana nuna masu saboda saka hijabi a kasar.

Tattakin nasu ya fi yin tasiri ne a biranen Accra da Kumasi da kuma Tamale, inda daruruwansu suka fito kan tituna dauke da kwalaye masu rubuce-rubucen yin kira ko dai ga hukumomi ko kuma ga al'umma baki daya.

Sun yi zargin cewa ana nuna masu wariya wajen daukar aiki, inda ake hana mata masu sanye da hijabi dama.

Daga cikin abin da matan ke dauke da shi a jikin kwalayen akwai: "Hijabi ba ya hana ni ayyuka", "hijabi akida ce a gare ni", "ku bar gashinku a bude ku kyale ni na saka hijabina" da sauransu.

Hakkin mallakar hoto @jabdulai
Image caption Sun ce 'yan sanda sun yi yunkurin dakatar da su duk da cewa an sanar da su kamar yadda doka ta tanada
Hakkin mallakar hoto @jabdulai
Image caption Wannan tana cewa ne "hijabi ba ya toshe mani kwakwalwa"

An yi ta amfani da maudu'ai irin su #HijabIsAnIdentity da #BeingMuslimInGhana a shafin Twitter domin bayyana ra'ayoyi daban-daban.

Hakkin mallakar hoto @DellyAisha
Image caption "Hijabi akida ce," in ji masu zanga-zangar

Wani mai suna Justice Okai-Allotey @Owula_Kpakpo cewa ya yi duk da cewa shi ba mutumin addini ba ne amma ya fahimci cewa duk bambancin ra'ayin da ke tsakaninka da mutum ya kamata ka girmama akidarsa.

Ita kuwa Aisha Delly Alabireh @DellyAisha cewa ta ce: "Hijabina ba ya barazana ga wani, saboda haka ku daina saka wa jikin mata ido."

Masu zangar sun yi ikirarin cewa 'yan sanda sun yi yunkurin dakatar da su duk da cewa an sanar da su kamar yadda doka ta tanada, sai dai ko a jikinsu.

Labarai masu alaka