Harin Masallaci: Mutum 15 sun mutu a Burkina Faso

Tuni aka tura jami'an tsaro a yankin bayan kai harin Hakkin mallakar hoto Getty Images
Image caption Tuni aka tura jami'an tsaro a yankin bayan kai harin

A kalla mutum 15 suka mutu, biyu kuma suka samu raunuka a wani harin bam da aka kai a wani masallaci da ke arewacin Burkina Faso.

'Yan bindiga ne suka afka wa wani masallaci da ke kauyen Salmossi a daren Juma'a a daidai lokacin da wasu ke sallah a cikin masallacin.

Harin ya jawo da dama daga cikin 'yan kauyen yin hijira wanda kauyen na kusa ne da iyakar kasar da Mali.

Daruruwan mutane ne dai aka kashe a kasar a sama da shekaru biyu da suka wuce inda ake zargin masu ikirarin jihadi da aikata kisan.

Wani daga cikin mazauna kauyen gorom-gorom ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa: ''Tun a safiyar yau ne mutane suka fara guduwa daga kauyen.''

Babu dai wata kungiya da ta dauki nauyin kai wannan hari.

Hare-haren masu ikirarin jihadi ya karu matuka a Burkina Faso tun a 2015, wanda hakan ya yi sanadiyar rufe dubban makarantu a kasar.

Rikicin ya bazu ne ta yankin iyakar kasar da Mali a inda masu ikirarin jihadin suka kwace ikon arewacin kasar tun a 2012 inda daga baya dakarun sojin faransa suka fatattake su.

Hukumar Kula da 'Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta bada kiyasin sama da mutum dubu 250 a Burkina Faso suka yi hijira cikin watanni uku da suka gabata sakamakon rikice-rikice.

A makon da ya gabata mutum 20 aka kashe a wurin hakar zinare a arewacin kasar.

Haka zalika a ranar Asabar, kusan mutum 1,000 suka yi zanga-zanga a Ouagadougou, babban birnin kasar domin nuna rashin jin dadinsu dangane da rikice-rikicen kasar da kuma yawaitar sojojin kawance na wasu kasashe da ke yankin kasar.

Labarai masu alaka