An kubutar da yaran da aka sace a Kano aka kai su Anambra

Kwamishinan 'yan sandan jihar kano CP Ahmed Iliyas tare da wasu da ake zargi da yin garkuwa da yara dahga kano zuwa jihar Anambra Hakkin mallakar hoto Kano Police
Image caption Kwamishinan 'yan sanda ya ce yaran sun shafe kusan shekara biyar a hannun masu garkuwar

Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta ce ta ceto wasu kananan yara 'yan asalin jihar kano da shekarunsu suka kama daga biyu zuwa 10 wadanda aka yi garkuwa da su a jihar Anambra da ke kudancin Najeriya bayan an sace su daga Kano.

Kwamishinan 'yan sandan jihar ta Kano Ahmad Ilyasu ya ce wasu daga cikin yaran harshensu ya sauya domin ko Hausa ba sa ji.

"Mun samu yara takwas zuwa 11 wadanda aka sace wasunsu harshensu ya juye ko Hausa ma ba sa ji kuma da ganin iyayensu yaran suka kama tsalle saboda sun kai shekara hudu ko biyar a hannun masu garkuwar," CP Ahmad Ilyasu ya shaida wa BBC.

Kwamishinan 'yan sandan ya ce sun samu nasarar gano yaran ne bisa sabon tsarin yaki da muggan laifuka da Sefeto Janar na 'yan sandan Najeriya ya fito da shi.

Wasu daga cikin iyayen yaran sun shaida wa BBC irin farin cikin da suka shiga saboda ganin yaran nasu.

"Na ji dadin da ba zai iya musaltuwa ba, na ji dadi na ji dadi. Na gode wa Allah. Allah ya kara masu karfin gwiwa, ya fito da sauran lafiya," wata uwa da ta samu danta ta bayyana.

Kazalika CP Ilyasu ya bayyana cewa sun kama masu manyan laifuka 124 ciki har da 'yan daba 99, inda suka kwace makamai da dama daga hannunsu.

Hakkin mallakar hoto kano Police
Image caption Daya daga cikin irin makaman da 'yan sanda suka kwace a hannun 'yan daba

Har wa yau, ya ce sun kama wasu masu garkuwar daban bayan sun saci wani yaro kuma suka bukaci a ba su kudin fansa naira miliyan 12.

"Ba su san cewa da 'yan sanda suke magana ba. Muka dauka muka ba su amma a cikin kudin akwai abin da muka saka ta yadda duk inda suka tafi muna ganin su.

"Muka yi ta hulda su har sai da suka kai mu Ningi, inda muka samo wannan yaro kuma muka kama su da kudin da muka ba su.

"Bayan an dawo da wannan yaro ne sai muka gano ashe wanda ake zargin makobcin mahaifin yaron ne."

Labarai masu alaka