Shugaban North Korea na rangadi bisa doki a wani tsauni mai daraja

This undated picture released by Korean Central News Agency on October 16, 2019 shows North Korean leader Kim Jong Un riding a white horse amongst the first snow at Mouth Paektu. Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Kim Jong-un bisa wani farin doki a tsaunin Paektu

Shugaba Kin Jong-un na Koriya ta Arewa ya hau tsauni mafi daraja a addinance bisa wani doki.

Ana iya ganin Shugaba Kim kan wani farin doki a cikin wasu jerin hotuna da kamfanin dillancin labarai na kasar suka fitar a tsaunin Paektu da dusar kankara ta lullube kamar bargo.

Ba wannan ne karo na farko da shugaban na Koriya ta Arewa ya hau tsaunin mai tsawon mita 2,750 ba.

Tsaunin na da daraja a tarihin kasar - kuma ana ganin a nan aka haifi tsohon shugaba Kim Jong-ol, wanda shi ne mahaifin Kim Jong-un.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Kim Jong-un bisa dokin a kan tsaunin Paektu mai daraja ga 'yan kasarsa
Hakkin mallakar hoto AFP

A shekarar 2017 ya hau tsaunin ana makonni kalilan kafin ya yi jawabinsa na sabuwar shekara. A wancan lokacin ne ya nemi a gyara dangantaka tsakanin kasashen Koriya biyu.

Rahotanni na cewa Mista Kim ya hau wannan tsaunin na Paektu har sau uku, kuma ya taba kai Shugaban Koriya ta Kudu, Moon Jae-in wurin a 2018.

Akwai kuma wannan hoton na kasa wanda ke nuna Mista Kim sanye da bakaken kaya da bakin takalmi a yayin wani hawa da yayi a shekarun baya.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Kim Jong-un bisa tsaunin na Paektu a wani lokaci da ya gabata

Labarai masu alaka