Macen farko da ta kai matsayin Air Warrant Officer a rundunar Sojin Saman Najeriya
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Macen farko mai babban matsayi a sojan saman Najeriya

Ku latsa hoton da ke sama domin ganin karramawar

A ranar Talata ne Shugaban rundunar Sojin Sama na Najeriya, Air Marshal Sadiqu Abubakar ya kara wa Master Warrant Officer Grace Garba girma zuwa Air Warrant Officer.

Wannan matsayin dai shi ne mafi girma da ba na hafsan sojin sama ba.

Grace Garba ce macen farko da ta kai matsayin nan a tarihin rundunar Sojin Sama.

Ta ce ta yi tsawon shekara 33 a rundunar, sannan ta yi shekara 25 a matsayi daya.

Ta yi godiya ga Allah da ya nuna mata wannan rana kuma ta yi kira da jama'a su yi aiki tsakaninsu da Allah.

Bidiyo: Fatima Othman