Haraji kan WhatsApp ya janyo zanga-zanga a Lebanon

A protester sits in front of flames in Dora, Lebanon Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Thousands have taken to the streets over the handling of an economic crisis

Ana ci gaba da zanga-zanga a Lebanon duk da gwamnatin kasar ta janye kudurinta na kakaba haraji kan kiran waya ta manhajar WhatsApp.

Gwamnatin ta bayyana cewa za ta fara saka haraji na dala 0.20 a kowace rana kan kiran waya da aka yi da manhajar WhatsApp da kuma wasu manhajojin.

Amma ta janye wannan kudirin nata sa'o'i kadan bayan arangamar da aka samu tsakanin jami'an tsaro da kuma masu zanga-zanga.

An ruwaito cewa gwamman mutane ne suka samu raunuka a ranar Alhamis bayan masu zanga-zanga sun kona tayoyi jami'an tsaro kuma suka harba hayaki mai sa hawaye.

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Daya daga cikin masu zanga-zanga da karensa

Me ya sa mutane ke zanga-zanga a Lebanon?

Dubban mutane ne a kasar suka afka tituna a daidai lokacin da kasar ke fuskantar matsin tattalin arziki wanda ake zargin gwamnatin kasar da haddasawa.

Wani akanta daga cikin masu zanga-zangar a birnin Beirut ya shaida cewa ''Ina zaune a gida sai na ga mutane na zanga-zanga ni ma sai na bi su.

''Ina da aure akwai kudaden da ya kamata a bani duk wata wanda nake bin gwamnati amma ba a bani ba, ga shi bana aiki, laifin gwamnati ne.''

Hakkin mallakar hoto EPA