Civilians pelt US army vehicles with potatoes in Syria
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Kalli yadda 'yan Syria ke jifan sojin Amurka da dankali

Dakarun Amurka sun sha jifa da dankali, inda fararen hula da ke jin haushin ficewar dakarun na Amurka daga Qamishi, birnin da Kurdawa ke da yawa a arewa maso gabashin Syria.

Mazauna yankin sun jefi motocin dakarun masu sulke a dai-dai lokacin da suke ficewa daga yankin bisa wata shawarar shugaba Donald Trump ta gaggawa domin janye sojojin kasar tasa daga yankin.

Ana yi wa shawarar shugaba Donald Trump ta janye sojojin nasa kallon wani mataki na share wa dakarun Turkiyya hanyar far wa Kurdawa.

Labarai masu alaka