Ba ni da hannu ba ni da mota amma ina kanikanci
Na'urarku na da matsalar sauraren sauti

Nura Adam:'Ba ni da hannu amma ina aikin kanikanci'

Ku latsa hoton da ke sama domin kallon bidiyon:

Nura Adam ba shi da hannaye da kafafu, haka Allah ya halicce shi. Amma hakan bai hana shi samun sana'a da zai kula da kansa da iyalansa ba.

Nura makaniki ne, yana gyaran babura da janerato, sannan yana koyarwa a makarantar Islamiyya.

Bugu da kari, Nura yana da difiloma a ilimin komfuta kuma yana da burin bude nasa kamfanin.

Bidiyo: Fatima Othman

Labarai masu alaka