APC: Buhari ya cancanci yabo kan rahoton bankin Duniya

Asalin hoton, Nigeria Presidency
Buhari ya sha yin kamfe da gyaran tattalin arziki yayin neman kuri'ar 'yan Najeriya
Jam'iyyar APC ta yaba wa gwamnatin shugaban Najeriya Muhammadu Buhari kan matakin da kasar ta kai a teburin da Bankin Duniya ya fitar na kasashen da bankin ke samun saukin huldar kasuwanci da su.
Kamar yadda bayanan Bankin Duniya na kasashen da suka fi sauki wajen yin kasuwanci na shekarar 2020 ya nuna, Najeriya a yanzu na mataki na 131 a duniya, inda ta tsallake kasashe 15 da a baya suke gabanta.
Bankin Duniyar ya ce Najeriya ta aiwatar da gyare-gyare wadanda suka hada da saukaka kulla yarjejeniya tsakaninta da kamfanoni.
"Hakan ya sa tattalin arzikin mutum miliyan 200 ya zama cikin mafiya kyau a duniya a jerin kasashen da suka samu ci gaba," in ji Bankin Duniya.
Kazalika, a ani sako nda ta aike wa manema labarai, APC ta yi maraba da yarjejeniyar da shugaban ya kulla da takwaransa na Rasha Vladimir Putin, a ci gaba da taron da ake yi tsakanin Rasha da kasashen Afrika.
A cewar jam'iyyar hakan zai karfafa dangantaka tsakanin kasashen biyu.
Habaka tattalin arziki na daga cikin alkawuran da gwamnatin APC ta yi wa 'yan Najeriya alkawari a shekarar 2015.